Zaben 2027: Aisha Yesufu Ta Janye daga Neman Takarar Sanata a Jam'iyyar NDC

Zaben 2027: Aisha Yesufu Ta Janye daga Neman Takarar Sanata a Jam'iyyar NDC

  • 'Yar gwagwarmayar kare hakkin bil'adama, Aisha Yesufu ta janye daga neman takarar sanata mai wakiltar Abuja a Majalisar dattawa
  • Hakan ya biyo bayan tsarin da jam'iyyar NDC ta amince da shi na fitar da 'dan takarar sanata ta masalaha, ba tare da shirya zaben fitar da gwani ba
  • Aisha ta bukaci magoya bayanta su kwantar da hankulansu, su maida hankali kan babban aikin da ke gabansu na ceto Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Fitacciyar mai fafutukar kare hakkin jama’a kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Aisha Yesufu, ta janye daga takarar kujerar Sanata mai wakiltar Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.

'Yar gwagwarmayar ta tabbatar da cewa ta hakura da neman takarar sanatar a karkashin jam’iyyar NDC gabanin babban zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

"A maido mani da kudi na," Matar da ta fito takarar shugaban kasa ta tada rigima a DLA

Aisha Yesufu.
Fitacciyar yar gwagwarmayar kare hakkin bil'adama, Aisha Yesufu Hoto: @AishaYesufu
Source: Twitter

Aisha Yesufu ta bayyana matakin nata ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, 29 ga watan Mayu, 2026.

Dalilin janyewar Aisha Yesufu daga takara

Ta ce jam’iyyar NDC ta yanke shawarar ba za ta gudanar da zaben fitar da gwani na kujerar Sanata a Abuja ba, wanda hakan ya sa ta janye daga shiga tseren neman tikiti.

“Jam’iyyarmu ta yanke shawarar ba za ta gudanar da zaben fitar da gwani na kujerar sanata a Abuja ba. Sai dai za ta gudanar da na kujerun majalisar wakilai,” in ji ta.

Aisha Yesufu ta aika sako ga magoya baya

Mai fafutukar ta bukaci magoya bayanta da su ci gaba da nuna hakuri tare da mayar da hankali kan abin da ta bayyana a matsayin babban burin ceto Najeriya a zaben shugaban kasa na 2027.

Ta ce:

“Ina rokon kowannenku da ku kwantar da hankalinku sannan ku mayar da hankali kan babban burin da muka sa a gaba, wato zaben shugaban kasa. Najeriya za ta samu sauyi mai kyau.”

Kara karanta wannan

Zargin fyade" ADC ta fara bore bayan kotu ta tasa 'keyar da takararta zuwa kurkuku

Aisha Yesufu ta kuma gode wa magoya bayanta na #AishaForSenate bisa goyon baya da jajircewar da suka nuna tun bayan bayyana aniyarta ta shiga takarar.

Ta kuma bayyana cewa a cikin mako mai zuwa za ta zagaya dukkanin kananan hukumomin yankin Abuja guda shida domin gode wa al’umma bisa irin tarbar da suka yi mata.

Jam'iyyar NDC.
Tutar jam'iyyar adawa a Najeriya ta NDC Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Yadda Aisha Yesufu ta shiga takarar sanata

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa Aisha Yesufu ta bayyana aniyarta ta neman kujerar Sanatan Abuja ne a ranar 6 ga watan Mayu 2026 bayan ta sauya sheka daga jam’iyyar ADC zuwa NDC.

A lokacin, ta bayyana cewa gogewarta a siyasa da kuma rawar da take takawa a cikin jam’iyyar ne suka karfafa mata gwiwar shiga takarar.

NDC ta fada cikin rikici a jihar Enugu

A wani labarin, kun ji cewa wani ɓangare na jam’iyyar NDC a jihar Enugu ya roƙi shugabancin ƙasa ya shiga tsakani kan rikicin shugabanci da ke neman kassara ta.

Jagoran ɓangaren, Dr. Johnpaul Anih, ya bayyana hakan ne ranar Litinin 25 ga watan Mayu, 2026 yayin wani taron manema labarai da ya gudanar.

Dr. Johnpaul Anih ya ce shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar da aka zaɓa ta hanyar sahihin taro, amma an samu masu kawo masa matsaloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262