An Sake Kai Wa Hausawa Hari a Kudancin Najeriya, an Rasa Rayukan Mutane

An Sake Kai Wa Hausawa Hari a Kudancin Najeriya, an Rasa Rayukan Mutane

  • Mutane uku sun mutu bayan wasu matasa sun kai hari kan unguwar Hausawa da ke Warri, jihar Delta, inda aka kuma wawashe shaguna
  • Mazauna yankin sun danganta rikicin da takaddama kan kuɗin harajin Naira 200 da ake karɓa daga masu adaidaita sahu
  • Wakilin Legit Hausa ya ji daga bakin shugaban yan Arewa da ke yankin ya bayyana damuwa kan yadda aka kai masu hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Warri, Delta - An samu asarar rayuka bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun farmaki unguwar Hausawa a jihar Delta.

An tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a unguwar da ke ƙaramar hukumar Warri ta Kudu a jihar, abin da ya janyo fargaba da lalacewar dukiyoyi.

An kai wa Hausawa hari a Delta
Sufeta-janar na yan sanda, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Rahotanni daga Daily Trust sun nuna cewa mutum ɗaya ya rasa ransa a ranar Litinin bayan wasu matasa daga yankin Igbudu Number One suka kutsa unguwar Hausawa tare da kai musu farmaki.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kai wa fitacciyar 'yar TikTok kuma 'yar Kwankwasiyya hari a Kano

Yadda aka kai wa Hausawa hari a Delta

Sai dai a safiyar Laraba, maharan sun sake dawowa, inda suka kashe wasu mata biyu tare da shiga gidaje da shaguna suna kwashe kayayyaki na miliyoyi.

Duk da cewa bayanan farko sun nuna mutane uku ne suka mutu, wasu mazauna yankin sun shaida cewa adadin waɗanda suka rasu ya kai huɗu, maza biyu da mata biyu.

Mazauna unguwar sun ce matsalar ta samo asali ne daga rashin jituwa kan kuɗin harajin kasuwa da na karɓar tikiti, musamman Naira 200 da ake karɓa daga masu baburan adaidaita sahu idan za su kai kaya cikin kasuwar Igbudu.

Sun yi zargin cewa wasu matasa da ke da alaƙa da al'ummar Igbudu Number One sun riƙa kutsawa unguwarsu, suna fasa ƙofofin gidaje, lalata kadarori da kwashe kayayyakin jama'a.

Bayan faruwar lamarin, jami'an tsaro sun bazama yankin domin hana sake barkewar rikici da kuma dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Yan bindiga sun banka wa gari wuta, sun ƙona mutane da ransu

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Delta, SP Bright Edafe, ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya bayyana cewa an cafke mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa rikicin yana da alaƙa da karɓar kuɗaɗen shiga ba bisa ƙa'ida ba, yayin da jami'ai ke ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya faru.

Rikici ya barke a Deltya, an kashe Hausawa
Taswirar jihar Delta da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Shugaban yan Arewa a yankin ya magantu

Wakilin Legit Hausa ya ji ta bakin Alhaji Mustapha Ogbonsu wanda ya ce ya yi magana da rundunar yan sanda bayan jin labarin abin da ya faru.

Ogbonsu ya ce sun yi magana da wadanda abin ya faru da su a unguwar Hausawa inda suka ce masa an tura yan sanda.

Ya ce:

"Abin da ya jawo wannan rikici shi ne maganar karbar haraji wanda ya juya zuwa fadan addini wanda ya jawo asarar rayuka da balla shaguna da gidajen Hausawa.
"Yan sanda sun yi kokarin cafke wasu daga ciki, muna kokarin ganin an zauna domin samun maslaha a matsayinmu na masu son zaman lafiya."

Kara karanta wannan

An kashe rayuka da aka tarwatsa 'yan Obi Kwankwaso a wajen kamfen

Ogbonsu ya bayyana cewa suna zaune tsawon shekaru da su ba tare da matsala ba saboda yadda suka shaku har akwai auratayya a tsakani.

An kai hari kan dan takarar gwamna

Mun ji cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya tsallake wani hari da ake zargin an shirya domin kashe shi a wurin kamfe a jihar Delta.

Mutane huɗu sun mutu, yayin da wasu huɗu suka samu munanan raunuka a harin da aka kai masa a Uduere, ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa.

Kwamitin kamfen y ce maharan sun yi ta harbi a kusa da sanatan, yayin da wani ganau ya tabbatar da cewa an harbi mutane a cikin taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.