Yadda Opay ke Turawa Mutane Tallafin N50,000 na Gwamnatin Tarayya
- Gwamnatin tarayya ta fara biyan tallafin N50,000 ga wasu 'yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa
- Shirin na bayar da tallafin ne ga iyalai matalauta da masu rauni a faɗin ƙasar, ta hannun kamfanonin hada-hadar kuɗi na zamani da gwamnati ta amince da su
- Masu amfani da OPay za su iya duba ko an zaɓe su ta hanyar lambar USSD ko manhajar kamfanin, ba tare da biyan kuɗin rajista ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta fara biyan tallafin kuɗi na N50,000 ga wasu 'yan Najeriya da ke fama da matsin tattalin arziki, ƙarƙashin shirin tallafin gaggawa da daidaita rayuwa na ƙasa.
An ƙaddamar da shirin ne ranar 30 ga Oktoba, 2026, domin taimaka wa iyalai matalauta da masu rauni waɗanda hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa suka fi shafa.

Source: Facebook
Daga cikin kamfanonin da aka amince su gudanar da biyan kuɗin akwai OPay, wanda ya bayyana hanyoyin da waɗanda aka zaɓa za su bi domin tabbatar da cancantarsu da karɓar tallafin a shafinsa na Facebook.
Bayanin da OPay ya yi
Ga matakan da masu amfani da OPay za su bi domin tantance ko an zaɓe su cikin waɗanda za su amfana da tallafin:
1. Buga lambar USSD: Buɗe wajen kiran waya, sannan ka buga *955*20 # ta amfani da lambar wayar da ka haɗa da asusunka na OPay.
2. Bi umarnin da aka bayar: Zaɓi amsar da ta dace, sannan ka bi matakan da za su bayyana domin duba cancantarka da karɓar tallafin.
3. Yi amfani da manhajar OPay: Haka kuma, za ka iya shiga manhajar OPay domin duba shafin farko ko an aiko maka da saƙon cewa an zaɓe ka.
4. Amincewa da karɓar tallafin: Idan aka zaɓe ka, bi umarnin da aka bayar domin tabbatar da amincewarka da kammala aikin.
5. Karbar kuɗin: Bayan kammala matakan, za a tura maka Naira 50,000 zuwa asusun walat ɗin wayarka da aka ware domin biyan kuɗin.
Opay ya yi gargadi
A bayanin da ya yi, kamfanin Opay ya gargadi jama'a da cewa ba a biyan ko sisi domin duba ko mutum ya cancanci samun tallafin.
Ya bukaci jama'a su yi taka tsantsan da masu damfara domin kaucewa fadawa tarkon su ko abin da ya yi kama da haka.
Opay ya bayyana cewa ba za a tambayi mutum lambobin sirri, ko wani abu na musamman ba daga wanda zai nemi duba ko ya cancanci karbar tallafin.

Source: Facebook
Gwamnati ta raba biliyoyi
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta kammala rabon Naira biliyan 75 ga masu masana'antu 104 domin ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida da bunƙasa tattalin arziki.
Haka kuma, gwamnati ta raba Naira biliyan 65.8 ga ƙananan 'yan kasuwa 15,018 domin faɗaɗa harkokinsu da samar da ayyukan yi.
Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Jumoke Oduwole, ce ta bayyana hakan, inda ta ce tallafin na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na bunƙasa harkokin kasuwanci a Najeriya.
Asali: Legit.ng

