Sanata Ya Ji Kalaman da Yan Bindiga Suka Faɗa Lokacin da Suka Bude Wa Tawagarsa Wuta
- Sanata Ovie Omo-Agege, ya ce maharan da suka kai wa tawagar kamfen ɗinsa hari a Delta sun riƙa ambaton sunansa tare da barazanar kashe shi
- Tsohon mataimakin shugaban Majalisar dattawan ya ce jami’an DSS da ke tare da shi ne suka taimaka masa ya tsira daga harin
- Omo-Agege ya bayyana cewa kusan mutane 15 sun jikkata, wasu daga cikinsu kuma sun samu munanan raunuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Delta, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, ya yi zargin cewa ’yan bindigar da suka kai wa tawagar kamfen ɗinsa hari a Jihar Delta, sun yi barazanar kashe shi.
Sanata Omo-Agegeg ya ce maharan sun riƙa ambaton sunansa tare da barazanar kashe shi yayin harin da ya yi sanadin mutuwar mutane huɗu.
Ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin wata hira da shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV, inda ya ba da labarin yadda maharan suka buɗe wuta jim kaɗan bayan ya fara yi wa magoya bayansa jawabi.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Mutane da dama sun mutu da aka yi yunkurin kashe sanata a wurin kamfe
Kalaman da yan bindigar suka faɗa
Omo-Agege, wanda ke takarar sanatan Delta ta Tsakiya a zaɓen 2027 a ƙarƙashin NDC, ya ce ya tsira daga harin ne saboda taimakon jami'sn DSS da ke yi masa rakiya.
Ya ce:
“A wurin taron, yayin da suke harbi, muna jin suna cewa, ‘Omo-Agege muke son kashewa. Dole ne mu kashe Omo-Agege.’
“Amma na yi sa’a saboda jami’an DSS da ke yi mini rakiya ƙwararru ne sosai. A gaskiya, bayan Allah, dalilin da ya sa nake raye a yau shi ne jami’an DSS da suke tare da ni.”
Ya yi zargin an jima da kitsa harin
Tsohon ɗan majalisar ya bayyana lamarin a matsayin harin da aka shirya tun da jimawa, inda ya yi zargin cewa akwai wasu abubuwa da suka faru kafin kai harin.
Ya kuma tambayi dalilin da zai sa a yi niyyar kashe shi alhali akwai wasu ’yan siyasa da ke neman kujerun zaɓe.

Kara karanta wannan
Kasurgumin ɗan bindiga ya tsallake tarkon sojoji, ya ci gaba da matsawa mutane a Zamfara
Omo-Agege ya ce maharan sun kai harin ne ƙasa da mintuna biyar bayan ya fara jawabi a wurin kamfen ɗin da ke Uduere, ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa a Jihar Delta.
Ya bayyana cewa ya matsa zuwa gefen motarsa ne domin ya samu damar kallon mutanen da ke cikin taron ido-da-ido, a lokacin ne aka fara harbe-harben.
“Allah ne Ya sa na tsira, ina cikin magana, sai na matsa zuwa gefen motar domin in iya kallon mutanen da nake yi wa jawabi ido-da-ido. Ina komawa, sai aka fara ruwan harsasai.”
A cewarsa, mutane huɗu daga cikin mambobin kwamitin kamfen ɗinsa sun mutu, yayin da kusan 15 suka jikkata, wasu daga cikinsu kuma suka samu munanan raunuka.
Yadda aka kai wa Omo-Agege hari
Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya tsallake wani hari da ake zargin an shirya domin kashe shi a wurin kamfe a jihar Delta.
Bayanai sun nuna cewa akalla mutane huɗu sun mutu, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka a harin da aka kai masa a Uduere, ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa.
Asali: Legit.ng