Opay, Moniepoint da Bankuna 5 da ke Tura Tallafin N50,000 a Najeriya

Opay, Moniepoint da Bankuna 5 da ke Tura Tallafin N50,000 a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen kamfanonin hada-hadar kuɗi guda biyar da ta amince da su domin gudanar da biyan tallafin N50,000 ga masu ƙaramin ƙarfi
  • Kamfanonin za su aika saƙonnin SMS ga waɗanda suka cancanta domin neman izininsu kafin tura kuɗin zuwa asusun bankunansu ko ta wayoyinsu
  • Gwamnati ta yi gargaɗin cewa waɗanda za su amfana ba sa buƙatar neman tallafin, biyan kuɗin rajista ko amfani da wakilai domin karɓar kuɗin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen kamfanonin hada-hadar kuɗi na zamani guda biyar da ta amince da su domin kula da biyan tallafin N50,000 na wata-wata ga 'yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi karkashin NERSI.

Kara karanta wannan

Yadda masu Opay za su iya karbar tallafin N50,000 duk wata na gwamnatin tarayya

An ƙirƙiri shirin ne domin rage wa al'umma raɗaɗin hauhawar farashin kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki, tare da tallafa wa iyalan da ke fama da tsadar rayuwa.

Moniepoint da Opay
Alamun Moniepoint da Opay. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dr Bernard Doro, ne ya sanar da fara biyan kuɗin cikin wata sanarwa da aka fitar ranar 30 ga Oktoba.

A cewar ministan, waɗanda suka cancanci tallafin za su samu saƙonnin SMS daga kamfanonin da aka amince da su domin neman izininsu kafin a tura kuɗin zuwa asusun bankunansu ko walat ɗin wayoyinsu.

Bankunan da za su tura kudin

Gwamnatin ta ce tana aiki tare da kamfanonin hada-hadar kuɗi na zamani masu lasisi domin tabbatar da cewa waɗanda suka cancanta sun karɓi kuɗinsu cikin tsaro.

Kara karanta wannan

Shin tallafin N50,000 da aka fara turawa 'yan Najeriya bashi ne ko kyauta? An samu bayani

Ga sunayen kamfanonin guda biyar da lambobin USSD ɗinsu:

  1. ALAT by Wema: *945*23#
  2. MoMo PSB: *671*0#
  3. NairaGram: *726*00#
  4. OPay: *955*20#
  5. Moniepoint: *557*327#

Doro ya bayyana cewa waɗanda suka cancanci tallafin za su samu sahihan saƙonnin SMS daga waɗannan kamfanoni, kuma dole ne su bayar da amincewarsu kafin a aiwatar da biyan kuɗin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ya ce:

Za a sanar da waɗanda za su amfana ta hanyar saƙon SMS daga kamfanin da aka amince da shi domin tabbatar da amincewarsu kafin a tura kuɗin kai tsaye zuwa asusun bankunansu ko walat ɗin wayoyinsu."

Gargadi kan 'yan damfara

Gwamnatin ta jaddada cewa waɗanda suka cancanci tallafin ba sa buƙatar cike takardar neman tallafi, biyan kuɗin rajista ko amfani da wasu mutane a matsayin masu shiga tsakani domin samun N50,000 ɗin.

Kara karanta wannan

Kamar Buhari, ana neman tallafa wa kamfen din ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027

Doro ya gargaɗi 'yan Najeriya kan masu damfara da za su iya amfani da tsarin biyan tallafin wajen yaudarar mutane.

Ya shawarci waɗanda za su amfana da su guji bayyana lambobin sirrinsu na banki (PIN) ko lambar tantance asusun banki (BVN) ga kowa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamnati ta tura tallafin kudi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta kammala rabon Naira biliyan 75 ga masu masana'antu 104 domin ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida da bunƙasa tattalin arziki.

Haka kuma, gwamnati ta raba Naira biliyan 65.8 ga ƙananan 'yan kasuwa 15,018 domin faɗaɗa harkokinsu da samar da ayyukan yi.

Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Jumoke Oduwole, ce ta bayyana hakan, inda ta ce tallafin na daga cikin shirin gwamnati na bunƙasa kasuwanci a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng