Maza Gumbar Dutse: Abin da Peter Obi Ya Yi da Aka Farmaki Tawagar NDC a Calabar

Maza Gumbar Dutse: Abin da Peter Obi Ya Yi da Aka Farmaki Tawagar NDC a Calabar

  • Peter Obi ya bayyana cewa ya ki daukar shawarar jami’an tsaronsa ta sauya hanya bayan samun rahoton cewa ana jifan ayarinsa a Calabar
  • ’Yan sanda sun ce sun hana rikici barkewa tsakanin magoya bayan NDC da APC a gaban otal ɗin Metropolitan da ke Calabar
  • Dan takarar shugaban kasar na NDC ya yi gargaɗin cewa ba za a bar irin waɗannan abubuwa su sake faruwa a zaɓen 2027 ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Calabar, jihar Cross River - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya bayyana yadda ya ƙi bin shawarar jami’an tsaronsa.

Peter Obi ya ki bin shawarar ne bayan samun rahoton cewa an kai hari kan magoya bayan jam’iyyar a Calabar, babban birnin Jihar Cross River.

Peter Obi ya yi magana kan harin NDC
Peter Obi na jawabi a wajen taron NDC Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Obi ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya fitar, inda yake ba da labarin abin da ya faru a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamban 2026 lokacin da ya kai ziyara birnin domin gudanar da taron tattaunawa da al’umma.

Kara karanta wannan

An bude wuta ga magoya bayan ADC yayin da Atiku ke kamfen a Sokoto

Yadda Obi ya ƙi sauya hanya

Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya ce an sanar da shi cewa wasu magoya bayan jam’iyyar APC na jifan ayarinsa da duwatsu bayan sun hango magoya bayan NDC.

Ya bayyana cewa jami’an tsaronsa sun ba shi shawarar bin wata hanya daban domin kauce wa wurin da ake samun tashin hankali.

Sai dai Obi ya ce ya ƙi amincewa da shawarar, inda ya yanke shawarar sauka daga motarsa domin ganawa da mutanen da abin ya shafa, jaridar The Punch ta kawo labarin.

A cikin bidiyon, ya ce:

“An gaya mini cewa wasu mutanen APC na jifan mutane da duwatsu, wasu kuma suna guduwa. Jami’an tsarona suka ba ni shawarar wata hanya daban, amma na ce musu, a Najeriya fa? Zan sauka na je na gan su.”

Ya ƙara da cewa kafin su fahimci abin da ke faruwa, waɗanda ake zargi da tada hankalin sun bar wurin.

Kara karanta wannan

ADC na neman darewa saboda takarar Atiku a 2027? An ji yadda zancen yake

Obi ya ɗora alhakin irin waɗannan abubuwa kan yadda ’yan Najeriya ke barin su faruwa, yana mai cewa ba za su amince da hakan ba a zaɓen 2027.

’’Yan sanda sun hana barkewar rikici

Rundunar ’yan Sandan Jihar Cross River ta ce ta yi nasarar hana wani rikici da ka iya barkewa tsakanin magoya bayan NDC da APC a Calabar.

Rahotanni sun ce magoya bayan NDC sun taru a gaban Otal ɗin Metropolitan da ke Calabar, inda aka shirya gudanar da taron tattaunawa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

A daidai lokacin, magoya bayan APC na gudanar da tattakin siyasa a kan hanyarsu ta zuwa ofishin gwamnan jihar.

Sai dai yanayin wurin ya sauya lokacin da magoya bayan APC suka tsaya a gaban otal ɗin, inda hakan ya jawo fargabar yiwuwar samun arangama tsakanin ɓangarorin biyu.

An farmaki tawagar NDC a Calabar
Taswirar jihar Cross River, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Peter Obi ya dauki alkawari

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya dauki gagarumin alkawari game da matsalar garkuwa da mutane.

Peter Obi ya sha alwashin shiga dazuzzuka domin ceto mutanen da aka sace idan aka zabe shi a shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng