An Jero Mutanen da za Su Yi wa Sarkin Daura Titsiye kan Zargin Taba Baturiya
- Gwamnatin jihar Katsina ta kafa kwamiti mai mutum tara domin gudanar da bincike kan zargin cin zarafin wata mata da ake yi wa Sarkin Daura, Alhaji (Dr.) Umar Farouk Umar
- Gwamna Dikko Radda ya amince da kafa kwamitin, wanda zai binciki zargin tare da gano hakikanin abin da ya faru a fadar Sarkin a kwanakin baya
- Rahoto ya nuna cewa kwamitin zai gabatar da rahotonsa ga gwamnati cikin mako huɗu kan abin da ake zargin Sarkin a shi bayan rantsar da mambobinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – Gwamnatin jihar Katsina ta kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan zargin cin zarafin wata mata da ake yi wa Sarkin Daura, Alhaji (Dr.) Umar Farouk Umar, CON.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Dakta Bala Salisu Zango, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ranar 25 ga Mayun 2026.

Kara karanta wannan
Gwamna ya karɓi rahoton abubuwan da aka gano kan mutuwar matasa 37 a ofishin NSCDC

Source: Facebook
Sanarwar da Ibrahim Kaulaha ya wallafa a Facebook ta ce Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ne ya amince da naɗin mambobin kwamitin domin su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Tsohon Alƙali zai jagoranci kwamitin
Gwamnatin jihar Katsina ta naɗa Mai Shari’a Amiru Sanusi mai ritaya a matsayin shugaban kwamitin binciken Sarkin Daura.
Sauran mambobin sun haɗa da mai ba gwamna shawara kan harkokin masarautu, Hon. Usman Abba; Mai Shari’a Sadiq A. Mahuta mai ritaya, Galadiman Katsina; da Kwamishinan Harkokin Addinai, Hon. Isah Dabai.
Haka kuma, akwai Alhaji Lawal Aliyu Daura; Farfesa Halima Kabir daga Sashen Harsuna da Al’adu na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya; da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Dakta Bala Salisu Zango.
Sauran mambobin su ne Hajiya Khadija Abdulkadir, mai ba Masarautar Belgium shawara kan diflomasiyyar tattalin arziki, da Babbar Lauya kuma Kwamishiniyar Shari’a ta jihar, Fadila Muhammad Dikko, wadda za ta zama sakatariyar kwamitin.
Ayyukan da aka ɗaura wa kwamitin
Daga cikin ayyukan kwamitin akwai binciken zargin cin zarafin da ake yi wa Sarkin Daura da gayyatar dukkan mutanen da ke da alaƙa da lamarin domin jin ta bakinsu.
Haka kuma, kwamitin zai gano ainihin dalilin da ya sa wani ɗan yawon buɗe ido ya ziyarci fadar Sarkin, tare da nazarin takardu, bayanai da duk wasu hujjoji da suka shafi zargin.
Gwamnatin ta kuma umarci kwamitin da ya tantance matakin alhakin da Sarkin ke da shi kan zargin, tare da ba da shawarwarin matakan hukunci da suka dace idan bincike ya tabbatar da laifi.

Source: Facebook
Baya ga haka, kwamitin zai gabatar da shawarwarin hanyoyin da za a bi domin hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
Sanarwar ta ce kwamitin zai fara aiki nan take bayan an rantsar da mambobinsa, sannan ya miƙa rahotonsa cikin makonni huɗu daga ranar ƙaddamar da aikinsa..
Radda ya gana da Sardaunan Daura
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Shugaba Bola Tinubu da marigayi Muhammadu Buhari ta ƙarfafa zumuncin Fadar Shugaban Ƙasa da al’ummar Daura.
Radda ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai gidan Sardaunan Daura, Alhaji Auwalu Umar Faruq, tare da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu–Dikko–Jobe.
A yayin ziyarar, gwamnan ya nemi addu’a da goyon bayan sarakunan gargajiya da al’ummar Daura ga ’yan takarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

