Amaechi: Abokin Takarar Atiku Ya Yi Tumu Tumu da Tinubu a Kamfen din ADC

Amaechi: Abokin Takarar Atiku Ya Yi Tumu Tumu da Tinubu a Kamfen din ADC

  • Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya zargi Tinubu da haddasa tsadar rayuwa, yunwa da talauci a Najeriya
  • Amaechi ya buƙaci ’yan Najeriya su kwatanta halin rayuwarsu a zamanin Muhammadu Buhari da na gwamnatin Tinubu
  • Tsohon gwamnan na Rivers ya ce yawan mutanen da suka halarci gangamin ADC a Sokoto ya nuna cewa jam’iyyar a shirye take domin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Tsohon gwamnan Jihar Rivers kuma mataimakin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rotimi Amaechi ya soki shugaban kasar ne kan tsadar rayuwa, yunwa da talauci da ake fama da su a Najeriya.

Amaechi ya ragargaji Tinubu
Chibuike Rotimi Amaechi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Rt Hon Chibuike Rotimi Amaechi, Bayo Onanuga
Source: Twitter

Amaechi ya bayyana Tinubu a matsayin shugaban ƙasa mafi muni da Najeriya ta taɓa samu, yayin da yake jawabi a wani gangamin yaƙin neman zaɓen ADC a jihar Sokoto, kamar yadda ya sa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi kwadagon da ya yi a Amurka don biyan kudin makaranta

Ya buƙaci ’yan Najeriya su kwatanta yanayin rayuwarsu a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu da lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Amaechi ya zargi Tinubu da tsananta rayuwa

Tsohon gwamnan ya ce matsin tattalin arziki, maimakon addini ko ƙabilanci, shi ne zai fi tasiri wajen yanke shawarar siyasar ’yan Najeriya a babban zaɓen 2027.

A cewarsa, matsalolin da jama’a ke fuskanta a yau sun shafi kowa ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

"A yau, siyasa ba ta ƙara shafar addini ko ƙabilanci ba. Abin da ake magana a kai shi ne tsadar rayuwa, yunwa da talauci. Mutum ɗaya ne ya jefa mu cikin wannan hali, sunansa Tinubu.
“Ku kwatanta rayuwarku lokacin da Buhari yake kan mulki da yadda kuke rayuwa a yanzu. Wanne ne ya fi kyau? Tinubu ne shugaban ƙasa mafi muni da Najeriya ta taɓa samu.
“Da yardar Allah, Tinubu zai ci gaba da kasancewa shugaban ƙasa mafi muni, domin bayan mulkinsa ba za a sake samun wani shugaban ƙasa da zai kai shi muni ba.” In ji shi.

Kara karanta wannan

An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu

Amaechi ya yaba da fitowar mutane

Da yake magana kan yawan magoya bayan da suka halarci gangamin ADC a Sakkwato, Amaechi ya bayyana cewa taron ya samu halartar jama’a da dama.

Ya ce irin wannan taron jama’a bai taɓa gani ba tun lokacin da suka zo yaƙin neman zaɓe a Sokoto a shekarar 2014.

A kalamansa, ya ce:

“Lokaci guda da na taɓa ganin irin wannan taron jama’a shi ne a shekarar 2014, lokacin da muka zo Sokoto domin yaƙin neman zaɓe. Ba a sake samun irin haka ba, har ma a shekarar 2019.
“Ko ba komai dai, mun nuna musu cewa a shirye muke domin zaɓen.”

Amaechi ya bayyana cewa yawan mutanen da suka fito yaƙin neman zaɓen ya nuna shirin da ADC take yi domin fafatawa a babban zaɓen 2027.

Alkawarin Atiku ga 'yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya gano hanyar da Tinubu zai samu kuri'u cikin sauki a 2027

Atiku ya kuma yi alkawarin buɗe iyakokin Najeriya domin kasuwanci da ƙasashe maƙwabta, tare da magance matsalar tsaro idan ya lashe zaɓen 2027.

Amaechi ya ragargaji Tinubu
Rotimi Amaechi na jawabi a wajen taron ADC a Sokoto Hoto: Rt Hon Chibuike Rotimi Amaechi
Source: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng