Shugaban APC Ya Gano Hanyar da Tinubu Zai Samu Kuri'u cikin Sauki a 2027

Shugaban APC Ya Gano Hanyar da Tinubu Zai Samu Kuri'u cikin Sauki a 2027

  • Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana ayyukan titin da gwamnatin Tinubu ke yi a matsayin babbar hujjar neman ƙuri’un al’umma a zaɓen 2027
  • Yilwatda ya ce ana gina titin Akwanga zuwa Jos da Gombe ne da nufin samar da hanya mai ɗorewa, wadda za ta iya kai wa sama da shekaru 100
  • Babbar hanyar Trans-Sahara za ta haɗa yankunan Kudu-maso-Kudu, Kudu-maso-Gabas, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas, tare da inganta tsaro da tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Nasarawa - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa ayyukan more rayuwa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke gudanarwa za su taimaka wa jam’iyyar wajen samun ƙuri’u a zaɓen 2027.

Yilwatda ya bayyana ayyukan a matsayin wata babbar hujja da ba za a iya ƙaryatawa ba wajen yaƙin neman zaɓen APC, yana mai cewa ’yan Najeriya za su iya tantance ayyukan gwamnati ta hanyar abubuwan da ta kammala a zahiri.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawar da shakkun 'yan Najeriya, ya fadi dalilinsa na runtumo basussuka

Shugaban APC ya yi maganar tazarcen Tinubu
Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi a wajen taro Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 31 ga watan Oktoban 2026 lokacin da ya kai ziyara domin duba yadda ake ci gaba da aikin gina sassan babbar hanyar Trans-Sahara da suka haɗa da Akwanga, Jos da Gombe.

Abin da gwamnatin Tinubu ke shirin cimmawa

Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta bayyana cewa ɓangaren hanyar da ya tashi daga Akwanga zuwa Jos yana da tsawon kilomita 125.

Wannan ɓangare na cikin babbar hanyar Akwanga-Jos-Bauchi-Gombe-Biu-Maiduguri, wadda aka tsara domin inganta zirga-zirga, tsaro da harkokin tattalin arziki a sassa daban-daban na Najeriya.

Da yake magana da manema labarai yayin ziyarar, Yilwatda ya jaddada muhimmancin aikin, inda ya ce ana gina hanyar ne domin ta daɗe sosai kafin a sake buƙatar gyara.

A kalamansa:

"Muna sa ran hanyar za ta iya ɗaukar sama da shekaru 100 kafin a fara tunanin sake yi mata gyara ko kula da ita. Wannan shi ne yadda ake gina abin tarihi mai ɗorewa.”

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: INEC ta fara fargaba kan zaben 2027

Hanyar za ta haɗa jihohi da dama

Shugaban APC ya ƙara bayyana cewa hanyar tana cikin wani babban shiri da ya taso daga Calabar, inda zai ratsa jihohi da dama kafin ya isa Jos.

Ya ce shirin ya haɗa da jihohin Ebonyi, Enugu da Benue, da kuma Abuja, kafin hanyar ta kai yankin Jos.

A cewarsa, babbar hanyar Trans-Sahara za ta kasance mai tsawon sama da kilomita 1,400, tare da haɗa yankuna huɗu na Najeriya.

Yankunan sun haɗa da Kudu-maso-Kudu, Kudu-maso-Gabas, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas, lamarin da ake sa ran zai inganta hulɗa da kasuwanci tsakanin al’ummomin yankunan.

Yilwatda ya ce aikin hanya shaida ce ta manufofin shirin Renewed Hope na gwamnatin Tinubu, yana mai cewa hakan ne zai sa ’yan Najeriya su ci gaba da mara wa shugaban ƙasa baya.

Nentawe ya yi magana kan tazarcen Tinubu
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Dogara ya kare Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara, ya bayyana cewa matsalolin tsaron da Najeriya ke fama da su sun samo asali ne tun kafin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hau mulki.

Dogara ya ce ta'addanci, tada kayar baya da ayyukan 'yan bindiga sun dade suna addabar kasar tun kafin shekarar 2023, lokacin da Tinubu ya zama shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng