Matakin da Kotu Ta Dauka a Kano Kan Kalubalantar Takarar Gwarzo a ADC

Matakin da Kotu Ta Dauka a Kano Kan Kalubalantar Takarar Gwarzo a ADC

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta ɗage sauraron ƙarar da ake ƙalubalantar takarar gwamnan NDC a zaɓen 2027
  • Lauyan NDC ya ce waɗanda suka shigar da ƙarar ba mambobin jam’iyyar ba ne, kuma ba su shiga zaɓen fitar da gwani da aka gudanar ba
  • Jam’iyyar ta nemi kotu ta yi watsi da ƙarar, tana mai cewa an shigar da ita ne bayan wa’adin kwanaki 14 da kundin tsarin mulki ya tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yi zama kan sauraron ƙarar da ke ƙalubalantar takarar gwamnan jam’iyyar NDC.

Kotun da ke jihar Kano ta dage sauraron karar har zuwa ranar 7 ga Disamba, 2026 da muke ciki.

Kotu ta yi zama kan shari'ar takarar gwamnan NDC
Dan takarar gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo. Hoto: Kwankwasiyya Reporters.
Source: Facebook

An dage shari'ar neman hana Gwarzo takara

An ɗage shari’ar ne bayan waɗanda suka shigar da ƙarar sun nemi ƙarin lokaci domin su mayar da martani kan ƙorafin farko da lauyan NDC, Barrista Magaji Mato, ya shigar yana neman kotu ta yi watsi da ƙarar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

2027: Kotu ta fatattaki karar da aka shigar da dan takarar ADC a Gombe

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman kotun na ranar Litinin, Mato ya ce masu ƙarar ba su shirya ci gaba da shari’ar ba saboda har yanzu ba su mayar da martani kan ƙorafin da sauran takardun da aka miƙa musu a makon da ya gabata ba.

Ya ce:

“Abin takaici, ɓangaren da ya kai mu kotu ya ce ba su shirya ba saboda mun shigar da wasu takardu, ciki har da sanarwar ƙorafin farko da ke neman kotu ta yi watsi da ƙarar tun a wannan mataki, saboda babu wata hujjar da za mu amsa.”

Lauyan ya ce shi da waɗanda yake karewa ba su yi adawa da buƙatar ɗage zaman ba.

A cewarsa, kotun ta amince da buƙatar tare da sanya ranar 7 ga Disamba domin sauraron shari’ar yadda ya kamata.

Mato ya ƙara da cewa suna shirye su mayar da martani idan aka miƙa musu takardun masu ƙarar, kuma za su kasance a shirye domin ci gaba da shari’ar a ranar da aka sanya.

Kara karanta wannan

PDP ta yi magana kan batun hada kai da su Atiku a kayar da Tinubu

Dalilan NDC na neman a yi watsi da ƙarar

Da yake bayyana dalilan ƙorafin farko da ya shigar, lauyan ya ce ƙarar ba ta cancanci a ɗauke ta a matsayin shari’ar da ta shafi zaɓen fidda gwani ba, saboda mutanen uku da suka shigar da ita ba mambobin NDC ba ne.

Ya kuma ce ko da a ce mambobin jam’iyyar ne, ba su shiga zaɓen fidda gwani na gwamnan da kwamitin gudanarwa na ƙasa na NDC ya shirya a ranar 29 ga Mayu, 2026 ba.

Mato ya bayyana cewa masu ƙarar ba su gabatar da takardun da ke nuna sun sayi fom ɗin takara ko kuma sun yi rajista a matsayin mambobin jam’iyyar ba.

Ya kira su da “mutanen haya da aka gabatar domin haddasa ruɗani tsakanin mutanen kirki na Jihar Kano”.

Haka kuma, lauyan ya kalubalanci lokacin da aka shigar da ƙarar, yana mai cewa an yi hakan ne bayan wa’adin kwanaki 14 da sashe na 285(9) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanada.

Kara karanta wannan

ADC ta gamu da cikas, kotu ta kori mutumin Atiku da ke takarar gwamna

Ya ce NDC ta miƙa sunayen ’yan takararta ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a ranar 10 ga Yuni, amma masu ƙarar sun shigar da ƙarar ne a ranar 17 ga Oktoba.

Abin da masu ƙarar ke nema

Mutane uku da ke ikirarin kasancewa mambobin NDC a Kano ne suka shigar da ƙarar, waɗanda suka haɗa da Garba Umar Isa, Yau Abubakar da wani mamba.

Suna neman kotu ta hana jam’iyyar tsayar da ɗan takarar gwamna a Kano domin zaɓen 2027.

Haka kuma, sun nemi kotu ta hana hukumar INEC wallafa sunan ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, bisa dogaro da hukuncin Kotun Ƙoli a shari’ar jam’iyyar Zenith Labour Party.

A zaman kotun da ya gabata, Mai Shari’a Simon Amobeda ya amince da shigar da ɗan takarar gwamnan NDC, Aminu Gwarzo, cikin waɗanda ake ƙara.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.