Yadda Obasanjo Ya Yi Kutun Kutun domin Hana Amaechi Zama Gwamnan Rivers
- Rotimi Amaechi ya bayyana yadda barazanar kama shi da Obasanjo ya yi ta tilasta masa barin Najeriya zuwa Ghana
- Tsohon gwamnan ya ce ya ci gaba da shari'arsa daga Ghana har kotu ta tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar PDP na gaskiya
- Amaechi ya bukaci matasan Najeriya su shiga harkokin siyasa domin samun damar zama gwamnoni, ministoci da sauran shugabanni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar
Abuja – Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya bayyana yadda barazanar kama shi da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi ta tilasta masa barin Najeriya zuwa Ghana a lokacin da yake fafutukar zama gwamnan jihar Rivers.
Amaechi ya ce Obasanjo ya yi ƙoƙarin hana shi zama gwamnan Rivers, inda ya bayyana cewa ya bar Najeriya ne bayan tsohon shugaban ƙasar ya yi barazanar sa a gaba a kama shi.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya yi wa kowane ɗan Najeriya addu'a a ziyarar da ya kai ƙasar Saudiyya

Source: Twitter
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a wanda PM News ta samu, Amaechi ya ce bai daina fafutukar neman haƙƙinsa ba duk da barin Najeriya, inda ya ci gaba da shari'ar daga Ghana har sai da ya samu nasara.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake kira ga matasan Najeriya da su ƙara himma wajen shiga harkokin shugabanci da siyasa domin kawo sauyi a ƙasar.
Amaechi ya bayyana yadda ya yi shari'a daga Ghana
Tsohon gwamnan ya ƙarfafa matasa da su yi amfani da yawansu wajen kawo sauyi a siyasar Najeriya, yana mai cewa za su iya zama gwamnoni, ministoci da sauran manyan shugabanni.
Ya kuma yi nuni da wata ƙasa da matasa suka taka muhimmiyar rawa wajen kifar da wani shugaba da ya daɗe a kan mulki, yana mai cewa matasan Najeriya ma za su iya cimma irin wannan nasara.
A kalamansa:
“Shugaba Obasanjo ya yi ƙoƙarin hana ni zama gwamna, amma za ku ga cewa ban zauna haka nan ba. Na tafi kotu, kuma lokacin da ya yi barazanar kama ni, sai na bar ƙasar.
“Na zauna a Ghana, kuma daga can na ci gaba da shari'ar har sai da na zama gwamna.”

Source: UGC
Yadda Amaechi ya zama gwamnan Rivers
Amaechi ya kuma yi bayanin rikicin shari'a da ya dabaibaye zama gwamna da ya yi a jihar Rivers, cewar rahoton Punch.
A cewarsa, duk da cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ce ta lashe zaɓen, kotu ta amince da shi a matsayin halastaccen ɗan takarar jam'iyyar, lamarin da ya buɗe masa hanyar zama gwamna.
Ya bayyana yadda ya zama gwamnan a matsayin wani abu da ba kasafai ake gani ba, saboda hukuncin kotu ne ya ba shi damar hawa kujerar, ba wai nasarar zaɓe kai tsaye ba.
Wike' ya lissafo matsalolin Atiku, Amaechi
Mun ba ku labarin cewa Nyesom Wike ya buƙaci Atiku Abubakar ya bayyana irin nasarorin da ya samu a shekaru takwas da ya yi mataimakin shugaban ƙasa.
Ministan ya ce shigar Rotimi Amaechi cikin ADC ta ƙara rikitar da fafatawar neman tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar.
Wike ya nemi a yi bayani kan kuɗaɗen wasu ayyukan da ake dangantawa da gwamnatin Amaechi a Rivers, ciki har da aikin layin dogo na cikin birni da aka ce ya lakume Naira biliyan 68.
Asali: Legit.ng
