Sanatan da Ya Tsallake Rijiya Ta Baya a Karo na 5 ana Neman Kashe Shi

Sanatan da Ya Tsallake Rijiya Ta Baya a Karo na 5 ana Neman Kashe Shi

  • Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya ce harin da aka kai wa gangamin siyasarsa a jihar Delta shi ne yunkuri na biyar na kashe shi
  • Omo-Agege ya zargi jami’an ’yan sanda da ke wajen taron da kin daukar mataki lokacin da ’yan bindiga suka bude wuta kan tawagarsa
  • A bayanan da ya yi bayan harin, dan takarar sanatan ya ce maharan sun jira sai ya mike domin fara jawabi kafin su fara harbe-harbe domin hallaka shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma dan takarar sanatan Delta ta Tsakiya a NDC, Ovie Omo-Agege ya bayyana harin da aka kai wa gangamin siyasarsa a jihar Delta a matsayin yunkuri na biyar na kashe shi.

Kara karanta wannan

Sanata ya ji kalaman da 'yan bindiga suka faɗa lokacin da suka bude wa tawagarsa wuta

Omo-Agege ya bayyana hakan ne ranar Talata, inda ya zargi jami’an ’yan sanda da ke wajen taron da kin daukar mataki yayin da wasu ’yan bindiga suka bude wuta kan tawagarsa a ranar Litinin.

Ovie Omo-Agege
Dan takarar da aka kai wa hari, Ovie Omo-Agege. Hoto: Ovie Omo-Agege
Source: Facebook

Bayanin da Omo-Agege ya yi

A hira da Channels TV, Omo-Agege ya ce harin farko da aka yi yunkurin kashe shi ya faru ne a wani taron tuntuba a al’ummar Usiefurun da ke karamar hukumar Ughelli South ta jihar Delta.

Ya bayyana cewa an hana su amfani da wasu wuraren taro, ciki har da makarantu da otal-otal, inda ya yi zargin ana yi wa masu otal barazanar soke musu lasisi idan suka ba su damar gudanar da taro.

Ya zargi ’yan sanda da kin kare shi

Omo-Agege ya zargi jami’an ’yan sandan da aka tura wajen gangamin da kallon yadda aka bude wuta ba tare da kokarin dakatar da maharan ba.

Ya ce jami’an sun tsaya suna kallon lamarin, duk da cewa ya kamata su hana harbe-harben, kwace makaman maharan tare da kama su.

Ya bayyana cewa abin da ya faru ya ba shi takaici, yana mai cewa bai yi tsammanin samun adalci daga jami’an da suka kasa kare shi ba.

Kara karanta wannan

Obi na zargin ana shirin alakanta shi da 'yan ta'adda don bata shi a Arewa

Taswirar jihar Delta
Taswirar jihar Delta a Najeriya.
Source: Original

Punch ta rahoto dan takarar sanatan ya ce maharan sun jira sai da ya mike domin fara jawabi kafin su bude wuta kan tawagarsa.

Omo-Agege ya kara da cewa hakan ya kara masa takaici, musamman ganin cewa jami’an tsaro suna wajen taron amma ba su yi kokarin hana harin ba.

'Yan sanda sun tabbatar da harin

A wani labarin, kun ji cewa rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane shida da jikkatar wasu da dama a harin da aka kai wa gangamin siyasar Ovie Omo-Agege a Ughelli North a jihar Delta.

Kakakin rundunar, CSP Ani Iniedu, ya ce Sufeto Janar na ’yan sanda, Olatunji Disu, ya umarci kwamishinan ’yan sandan jihar da ya gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Gwamnatin jihar Delta ta kuma sanya dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a duk fadin karamar hukumar Ughelli North har sai ta ba da wani sabon umarni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng