An Fara Batun Tinubu Ya Je Umrah ne don Neman Kuri'un 'Yan Arewa, Hadiminsa Ya Magantu
- Ademola Oshodi ya ce ziyarar Umrah da Tinubu ya kai Saudiyya ibada ce, ba wani yunƙuri na neman goyon bayan masu zaɓe a Arewa ba ne
- Ya bayyana cewa samun damar shiga cikin Ka’aba wata babbar dama ce da Musulman Najeriya suka ji daɗinta, ba wai al’amarin siyasa ba
- Oshodi ya shawarci sauran ’yan takarar shugaban ƙasa da su ma su nemi shiriya daga Allah, maimakon siyasantar da ibadar Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani hadimin shugaban ƙasa, Ademola Oshodi, ya yi watsi da ra’ayoyin da ke cewa ziyarar ibadar Umrah da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai Saudiyya na da manufar neman goyon bayan al’ummar Arewacin Najeriya gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Oshodi, wanda shi ne babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin ƙasashen waje, ya ce ya kamata a kalli ziyarar daga mahangar addini da ƙasa baki ɗaya, ba wai a matsayin wani yunƙuri na rinjayar masu zaɓe a wani yanki ba.

Kara karanta wannan
Shugaban APC ya ji dadin giyar mulki, ya cika baki kan girman jam'iyyar a Najeriya

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamban 2026 yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels tv.
Damar shiga Ka’aba ba batun siyasa ba ne
Hadimin shugaban ya ce muhimmancin damar da Tinubu ya samu na shiga cikin Ka’aba, wadda ita ce mafi tsarkin wuri ga Musulmi, ya wuce batun siyasar yankuna.
A cewarsa, Musulman Najeriya daga sassa daban-daban na ƙasar sun ji daɗin wannan dama ta musamman da aka bai wa shugaban.
Oshodi ya ce ra’ayoyin jama’a ba abu ne da za a iya haɗawa wuri guda ba, don haka bai dace wani ɓangare na al’umma ya ce ziyarar na neman ƙuri’un Arewa ba.
Ya ƙara da cewa Tinubu shi ne shugaban farko daga yankin Kudu maso Yammacin Najeriya da aka ba irin wannan karramawa, don haka ya kamata a duba yadda hakan ya shafi al’ummar yankin da kuma ƙasar baki ɗaya.
“Ba batun Arewa ko Kudu kawai ba ne. Batun Musulunci ne, kuma Musulman Najeriya sun ji daɗin wannan dama. Bugu da ƙari, ba batun siyasa ba ne.” In ji shi.
Tinubu ya sha zuwa aikin Umrah da Hajji
Oshodi ya bayyana cewa Tinubu ya sha zuwa aikin Umrah da Hajji a lokuta daban-daban a rayuwarsa, don haka bai kamata a ɗauki ziyarar da ya kai a wannan karon a matsayin wani sabon salo na siyasa ba.
Ya ce an ba shugaban wannan dama ta musamman ne saboda shi ne jagoran ƙasa mafi yawan Musulmi a nahiyar Afirka.
Ya kuma yi kira ga jama’a da kada su fi mayar da hankali kan lokacin da aka gudanar da ziyarar, maimakon duba muhimmancin ibadar da kuma neman shiriyar Allah.
An ba sauran ’yan takara shawara
Hadimin shugaban ya ce abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne Tinubu ya je neman taimakon Allah kan yadda zai jagoranci Najeriya da kuma samun nasara a ƙoƙarinsa na sake zaɓe.
Ya kuma shawarci sauran ’yan takarar shugaban ƙasa da su bi irin wannan hanya ta neman shiriyar Allah, ko ta hanyar zuwa Kudus ko Makka.
Oshodi ya ce bai kamata ’yan siyasa su riƙa mayar da dukkan abubuwan da suka shafi rayuwa da addini zuwa batun siyasa ba.

Source: Twitter
Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya addu'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kammala ziyarar da ya kai kasar Saudiyya domin yin ibada da addu'o'i ga Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya ce ya yi addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da wadata ga Najeriya da al’ummarta a yayin ziyarar da ya kai Masarautar Saudiyya.
Asali: Legit.ng

