Tinubu Ya Fadi Kwadagon da Ya Yi a Amurka don Biyan Kudin Makaranta
- Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya ce ya yi aikin tuƙin tasi da wasu ayyuka a Amurka domin tara kuɗin karatunsa a jami'a
- Shugaban ƙasar ya bayyana cewa abubuwan da ya fuskanta sun sa ya fahimci ƙalubalen da ɗalibai ke fuskanta wajen biyan kuɗin makaranta da masauki
- Ya ce NELFUND ta bayar da rancen kudin karatu sama da Naira biliyan 372 domin taimaka wa ɗaliban manyan makarantu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana yadda ya yi aikin tuƙin tasi da wasu ayyuka daban-daban a Amurka domin tara kuɗin da zai biya karatunsa a jami'a.
Tinubu ya ce bayan isa Amurka, ya shafe watanni yana aiki da tara kuɗi kafin ya fara karatu, saboda ba shi da isassun kuɗaɗen da zai biya bukatunsa na makaranta.

Source: Twitter
Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamban 2026 yayin da yake bayyana nasarorin gwamnatinsa a ɓangaren ilimi.
Tinubu ya yi aiki domin biyan kuɗin karatu
A cikin saƙon nasa, Tinubu ya ce lokacin da ya fara zuwa Amurka tun yana saurayi, ya yi aikin tuƙin tasi domin samun kuɗin karatunsa.
Ya bayyana cewa har sai da ya ɗage fara karatunsa na tsawon wasu watanni domin ya samu damar tara isassun kuɗaɗe.
Tinubu ya ce daga baya, lokacin da ya isa birnin Chicago, ya riƙa gudanar da ayyuka daban-daban domin samun kuɗin kula da kansa da kuma biyan kuɗin karatunsa a jami'a.
"Na san abin da yake nufi mutum ya damu da yadda zai biya kuɗin makaranta, na masauki da kuma sauran buƙatunsa, a daidai lokacin da yake neman ilimi.
“Waɗannan abubuwan da na fuskanta sun ci gaba da kasancewa a raina. Na san irin damar da ilimi ya buɗe mini a rayuwata, kuma na yi imanin cewa duk wani yaro ɗan Najeriya ya cancanci samun irin wannan dama, ba tare da la’akari da inda aka haife shi ko kuɗin da iyayensa suke da shi ba.” In ji shi.
Tinubu ya fadi abin da gwamnatinsa ta sa gaba
Shugaban ƙasar ya ce ilimi na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta ba muhimmanci, yana mai cewa tana ƙoƙarin faɗaɗa damar samun ilimi ga yaran Najeriya.
Ya bayyana cewa Asusun Ba da Lamunin Karatu na Ƙasa (NELFUND) ya bayar da rancen karatu sama da Naira biliyan 372 domin taimaka wa ɗalibai wajen biyan kuɗaɗen makaranta da sauran bukatunsu.
Yadda aka kafa NELFUND
An kafa NELFUND ne ƙarƙashin dokar ba da lamunin karatu ga ɗalibai domin samun damar zuwa manyan makarantu ta shekarar 2024.
Tinubu ya sanya hannu kan dokar a watan Afrilun 2024, domin samar da tallafin kuɗi marar ruwa ga ɗaliban Najeriya da suka cancanta a manyan makarantun gwamnati.
Tsarin ya tanadi taimaka wa ɗalibai wajen biyan kuɗin makaranta da kuma samun kuɗin gudanar da rayuwarsu yayin da suke karatu.

Source: Twitter
Sauye-sauyen Tinubu sun amfani attajirai
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atedo Peterside, wanda ya kafa bankin Stanbic IBTC Bank Plc da gidauniyar Anap Foundation, ya yi magana kan sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu.
Atedo Peterside ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu sun fi amfani ga masu hannu da shuni, yayin da suka ƙara tsananta halin rayuwar miliyoyin ’yan Najeriya.
Asali: Legit.ng

