Jerin Labaran Karya da Suke Yawo a Yanar gizo da Za a Iya Dauka Gaskiya ne

Jerin Labaran Karya da Suke Yawo a Yanar gizo da Za a Iya Dauka Gaskiya ne

Abuja - A kokarinmu na fito da labarai marasa inganci, mun tattaro wasu kanzon kuregen da suka yi ta yawo kwanan nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Mun tattaro labaran bogin da suka karade dandalin sada zumunta da sauran kafofi a makon karshe na watan Oktoban 2026.

Legit Hausa ta yi nusto a kafofin sadarwa da shafuka da gidajen jaridu, ta fito da manyan labaran karya da aka saki a makon nan.

Kamfen APC
Gwamnonin Arewa wajen bude kamfen APC Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Labaran karya a makon nan

1. N2.3tr wajen shirya kamfen APC

Wata takarda ta rika yawo a shafukan Facebook da makamantansu, ana cewa APC ta kashe N2.3tr domin shirya taron kamfe.

Bola Tinubu ya soma yakin neman zaben shi da Kaduna, takardar ta yi ikirarin su Abdulaziz Yari sun batar da Naira tiriyan 2 a nan

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ba da mamaki, ya dauki alkawari shiga dazuka da afafunsa

Dole kwamishinan labarai da al’adu a Kaduna, Ahmed Maiyaki ya fitar da jawabi domin karyata wannan zance mara tushe.

Maiyaki ya ce tun a wurin rubuta suna za a san labarin karya ne kuma ba a ware kudin ba, asali ba jihar ba ta da wannan kudi.

2. Tinubu zai iya mutuwa saboda zabe

Wani hoto dauke da tambarin APC Hausa ya yi ta yawo a shafin Facebook cewa Bola Tinubu ya ce zai iya mutuwa saboda zabe.

An yi karyar shugaban kasar ya ce: “Zan iya rasa rai na idan na fadi zabe.”

Legit Hausa ta bincika ta gano cewa babu inda shugaban Najeriyan ko wani daga cikin masu magana da yawunsa ya fadi haka.

An duba shafukan APC da na fadar shugaban kasa ba a samu zancen ba, haka mun tabbatar da cewa karya ne ta kafar Polihive.

3. Harajin 25% a Najeriya

Sanata Ireti Kingibe mai wakiltar birnin Abuja a Majalisar Dattawa ta ce za a rika cire 25% daga abin da mutane suka samu.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya sake taso Bola Tinubu a gaba, ya fadi shirmen da ya yi

An rahoto sanatar ta ADC tana fada wa jama’a cewa abokan aikinta sun amince da kudirin karbar harajin kuma zai yi aiki bayan zabe.

Fact Check Africa ta yi duba game da wannan batu kuma ta gano cewa babu kanshin gaskiya a maganganun sanatar adawar.

A dokar haraji ta 2025, babu sashen da ya wajaba wa mutane cire 25% na duka abin da suka samu, su ba hukuma da sunan haraji.

4. Kirkirar hotuna wajen taron APC

Saboda a kashe wa jam’iyya mai-ci kasuwa, wasu sun rika kirkirar hotunan karya, suna cewa taron yakin zaben APC bai yi armashi ba.

A zahirin gaskiya kuwa, dinbin mutane ne suka halarci gangamin da APC ta shirya domin bude yakin zaben sugaban kasa a 2027.

Za a ga irin wadannan hotuna a shafin ADCVangaurd_a kafar X, ana cewa hotunan da suke nuna an cika a taron APC na bogi ne.

An cika Kaduna a ranar, amma duk da haka ZeroGPT ya tona yadda wasu sun rika yada hotunan karya da aka kirkiro da fasahar AI.

Kara karanta wannan

Ziyarar Hannatu Musawa ofishin uban ‘ya ‘yanta, Abdussamad ya dawo da batun aure

Labaran bogi: Yadda aka yi wa Opay sharri

A karshen Agusta, an karanta rahoton yadda labaran kanzon kurege sula cika shafukan sada zumunta da shafuka na yanar gizo.

Rahoton nan ya tattaro karyayyakin da muka ci karo da su a a Facebook, WhatsApp, da X wadanda har suk jawo aka yi ram da wasu.

A sahun labaran karyan da suka yi fice akwai batun cewa kamfanin Opay zai bar aiki, haka ya sa mutan suka yi ta cire kudi daga bankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng