Ruɗani: INEC Ta Dora NDC amma Babu Sunan Aminu Gwarzo a Jerin Yan Takarar Gwamnan Kano

Ruɗani: INEC Ta Dora NDC amma Babu Sunan Aminu Gwarzo a Jerin Yan Takarar Gwamnan Kano

  • Hukumar zaben Najeriya watau INEC ta sanya jam'iyyar NDC cikin jam'iyyu 20 da za su fafata a zaɓen gwamnan Kano na 2027
  • NDC ita ce jam'iyya ta 13 a cikin jerin jam'iyyun da hukumar ta amince su tsayar da 'yan takara babban zabe mai zuwa da za a yi a watan Fabrairun 2027
  • Sai dai hukumar ba ta bayyana sunan Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar NDC ba, tana mai cewa hakan ya biyo bayan umarnin kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya jam'iyyar NDC cikin jerin jam'iyyun da za su fafata a zaɓen gwamnan jihar Kano da za a gudanar a watan Fabrairun 2027.

Binciken da Legit Hausa ta yi ya nuna hukumar zaɓen Najeriya ta aanta NDC a matsayin jam'iyya ta 13 cikin jam'iyyu 20 da INEC ta amince su tsayar da 'yan takara a zaɓen gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

"Yadda cire sunan Aminu Gwarzo da INEC ta yi ya zama alheri ga NDC a jihar Kano"

Aminu Gwarzo.
Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin iniwar jam'iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo Hoto: Aminu Abdussalam Gwarzo
Source: Facebook

Hakan na kunshe a jerin sunayen jam'iyyu da yan takarar gwamnan Kano da za su fafata a zaben 2027, wanda INEC ta yi wa gyara kuma ta wallafa a shafinta na yanar gizo da safiyar yau Asabar, 31 ga watan Oktoba, 2026.

INEC ba ta dora sunan Aminu Gwarzo ba

Sai dai sabanin jihar Gombe, inda hukumar ta bayyana sunan Farfesa Pantami a matsayin ɗqan takarar gwamna na NDC, a jerin sunayen 'yan takarar jihar Kano, sunan jam'iyyar NDC kawai aka bayyana.

Hukumar ba ta bayyana sunan Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Kano ba.

A ƙarshen bayanin da ta fitar, hukumar INEC ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon wani umarnin kotu.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262