Gwamna Abba Ya Aika wa Kwankwaso Sako da Ya Cika Shekaru 70 da Haihuwa

Gwamna Abba Ya Aika wa Kwankwaso Sako da Ya Cika Shekaru 70 da Haihuwa

  • Abba Kabir Yusuf, ya fitar da jawabi domin taya Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 70 a ban kasa
  • Mai girma gwamnan ya yaba da gudunmawar Kwankwaso wajen ci gaban jihar Kano, siyasa da dimokuraɗiyya
  • Ya roƙi Allah SWT Ya ƙara wa tsohon gwamna lafiya, tsawon rai da ƙarfin ci gaba da yi wa al'umma hidima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya taya Rabiu Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa a duniya.

Mai girma gwamnan ya zabi wannan lokaci ya taya tsohon mai gidansa kuma tsohon gwamnan jihar Kano murnar wannan rana.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yana gaida jama'a Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Abba Kabir Yusuf ya taya Rabiu Kwankwaso murna

Sakon ya fito ne ta bakin Darekta na sashen yada labarai na gidan gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna Inuwa, Sanata Danwambo sun hadu a jana'iza kasa da wata 3 kafin gwada kwanji a zabe

A yau Laraba, 21 ga watan Oktoba 2026, Rabiu Kwankwaso ya cika shekaru 70 da haihuwa.

A jawabin Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, an ji Abba Kabir yana yabon gudumuwar da Kwankwaso ya bada a Kano da kasa.

Yake cewa ranar 21 ga Oktoba lokaci ne na musamman da ake amfani da ita domin waiwayen cigaban da ya kawo wa jihar Kano.

Jawabin taya Kwankwaso murnar cika shekara 70

Sanarwar ta ce:

"Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, murnar cika shekaru 70 da haihuwa.
"Gwamna Yusuf ya bayyana wannan rana a matsayin wata muhimmiyar dama ta bikin rayuwar Sanata Kwankwaso, jagorancinsa da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Jihar Kano da Najeriya.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Dattijon ƙasa kuma jagoran ƙungiyar Afenifere ta Najeriya ya rasu

"Gwamnan ya yaba da rawar da Kwankwaso ya taka wajen bunƙasa harkokin siyasa a jihar.

Dawakin Tofa ya kara da cewa:

"Ya ce wannan ranar haihuwa ta ba da damar yin waiwaye kan shekarun da tsohon gwamnan ya shafe yana yi wa al'umma hidima. Haka kuma, ta ba da damar duba gudunmawarsa wajen tafiyar da mulki, bunƙasa abubuwan more rayuwa da faɗaɗa shigar jama'a cikin harkokin dimokuraɗiyya a Jihar Kano."

Kakakin na gwamnan jihar Kano ya yi addu’a ga Allah Sarki SWT ya ƙara wa Rabiu Kwankwaso lafiya da nisan kwana a duniya.

"Gwamna Yusuf ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba tsohon Ministan Tsaro, Mai Girma Sanata Kwankwaso, lafiya, tsawon rai da ƙarin ƙarfi domin ya ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Lokacin tafiya ya yi: Tsohon gwamna a Najeriya ya rasu yana da shekaru 71 a duniya

"Ya kuma yi masa fatan ƙarin shekaru cikin zaman lafiya da farin ciki yayin da yake murnar wannan gagarumar nasara ta rayuwa.
"Barka da cika shekaru 70 da haihuwa, Ran ka ya dade!"

- Sanusi Bature Dawakin Tofa

Bashir Ahmad zai yi wa Abba aikin kamfe

Labari ya zo cewa Bashir Ahmad ya zama Darektan kwamitin yada labarai na zamani wajen tallar APC a a zaben jihar Kano na 2027.

Tsohon hadimin na Muhammadu Buhari zai jagoranci tallar Abba Kabir Yusuf a kafofin sadarwa na zamani tare da wasu matasa.

‘Dan siyasar da ya nemi zama 'dan takaran majalisa zai yi aikin kamfe tare da irinsu Ibrahim Adam, Musayyib Ungogo da Amir Kima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng