Yadda Cire Sunan Aminu Gwarzo da INEC Ta Yi Ya Zama Alheri ga NDC a Jihar Kano

Yadda Cire Sunan Aminu Gwarzo da INEC Ta Yi Ya Zama Alheri ga NDC a Jihar Kano

  • Aminu Abdussalam Gwarzo ya ce cire sunansa daga jerin ’yan takarar INEC da aka yi da farko ya ƙara wa NDC farin jini a Kano
  • Ya ce rade-radin dawo da sunansa cikin jerin ya tabbatar da cewa jam’iyyar NDC ta cika dukkan ƙa’idojin zaɓe
  • NDC ta ce za ta ci gaba da neman goyon bayan jama’a a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano gabanin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na NDC, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya ce jam'iyyarsu ta kara farin jini da yawan magoya baya.

Gwarzo ya ce cire sunansa daga jerin ’yan takarar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da farko, ya ƙara wa jam’iyyar farin jini tare da jawo mata ƙarin magoya baya gabanin zaben Kano na 2027.

Kara karanta wannan

Abba Hikima ya fito da abin da ya kamata mutane su sani kan takarar Pantami da Aminu Gwarzo

Aminu Gwarzo.
Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jam'iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo Hoto: Comr Aminu Abdulsalam Gwarzo
Source: Facebook

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana haka ne jim kadan bayan an fara yada labarin cewa INEC ta dawo da sunansa cikin jerin yan takara, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Aminu Gwarzo ya ce dawo da sunansa bayan rahotannin da suka nuna cewa INEC ta amince da takararsa da kuma ta ɗan takarar gwamnan PDP a jihar Gombe, Farfesa isa Pantami, ya tabbatar da cewa NDC ta cika dukkan ƙa’idojin zaɓe.

NDC ta cika duka sharudda

Mai magana da yawun Gwarzo, Ibrahim Garba Shuaibu, ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan lamarin.

Ya ce jam’iyyar ba ta taɓa tsorata da cire sunan ɗan takararta da aka yi da farko ba, domin ta bi dukkan hanyoyin da aka shimfiɗa.

Ya ce jam’iyyar ta gudanar da rajistar mambobinta, zaɓen fitar da gwani da kuma miƙa bayanan ɗan takararta bisa ƙa’idojin zaɓe da suka dace.

Kara karanta wannan

NDC tana sauraron INEC da aka shiga rudu game da takarar Aminu Abdussalam a Kano

A cewarsa, rigimar da wasu ke ganin za ta raunana jam’iyyar, a maimakon haka, ta jawo hankalin jama’a, tausayi da ƙarin goyon baya ga NDC.

“Abin da wasu suka yi tunanin zai raunana mu, a maimakon haka, ya ƙara jawo mana hankalin jama’a tare da ƙarfafa tushen goyon bayanmu. Rigimar ta sa mutane da dama suka ƙara sha’awar sanin jam’iyyarmu, ɗan takararmu da kuma abin da muke wakilta,” in ji shi.
NDC .
Tutar jam'iyyar adawa a Najeriya watau NDC Hoto: NDC Kwankwasiyya
Source: Facebook

NDC ta ƙara samun kwarin gwiwa

Shuaibu ya ƙara da cewa dawo da sunan Gwarzo, duk da ba a fada masu a hukumance ba, ya ƙara wa jam’iyyar kwarin gwiwa kan tsarin zaɓe tare da ƙarfafa aniyarta ta shiga takarar zaɓen 2027.

Ya jaddada cewa lamarin ba zai ɗauke hankalin jam’iyyar daga harkokin siyasarta ba, inda ya ce babban abin da ta sa a gaba shi ne wayar da kan jama’a da neman goyon bayansu a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Abba Hikima ya soki INEC

Kun ji cewa lauya mai kare hakkin ɗan Adam, Abba Hikima, ya buƙaci INEC ta nemi afuwar Isa Ali Pantami, Aminu Gwarzo da sauran ’yan takarar da ta cire sunayensu.

Ya kuma buƙaci hukumar ta biya waɗanda abin ya shafa diyya, yana mai cewa babu wani abin yabawa a matakin da INEC ta ɗauka na dawo da sunayen ’yan takarar bayan cire su da farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262