NDC Tana Sauraron INEC da Aka Shiga Rudu game da Takarar Aminu Abdussalam a Kano

NDC Tana Sauraron INEC da Aka Shiga Rudu game da Takarar Aminu Abdussalam a Kano

  • An rasa gane makomar takarar Aminu Abdussalam Gwarzo, jam'iyyar NDC tana jiran bayani daga INEC
  • Shugaban jam’iyyar NDC a Kano ya ce jami’an INEC sun fada masa ya jira sanarwar da za su fitar tukuna
  • Husseini Mairiga ya ce za su ci gaba da yaƙin neman zaɓe da zarar INEC ta karbi korafinsu a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Shugaban jam’iyyar NDC na jihar Kano, Husseini Mairiga, ya bayyana farin cikinsa kan rahotannin takara da suke samu.

Ana cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da ɗan takararta na gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Aminu Abdussalam
Aminu Abdussalam mai neman gwamnan Kano a NDC tare da masoya da ya dawo daga Umran Hoto: Hamza Ahmad Telan Mata
Source: Facebook

Ana cewa NDC za ta shiga zaben Kano

A ranar Juma’a da safe, Leadership ta rahoto cewa NDC ba ta da tabbacin an karbi korafinta game da zaben gwamnan jihar Kano.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, INEC ta amince da takarar Sheikh Pantami da Aminu Gwarzo a zaɓen 2027

Babu bayani a hukamance zuwa yanzu daga INEC cewa ta amince Aminu Abdussalam ya tsaya takarar gwamna a zaɓen 2027.

Kano: Jam'iyyar NDC tana jiran sanarwa daga INEC

Husseini Mairiga ya ce jam’iyyar NDC na jiran sanarwar INEC a hukumance kafin tabbatar da sahihancin labarin da yake yawo.

Da yake zantawa ta wayar tarho, shugaban jam’iyyar ya bayyana rahotannin saka sunan ‘dan takaransu a matsayin abin farin ciki.

Amma ya ce jami’an INEC sun shawarce shi da ya jira sanarwar da hukumar za ta fitar ranar Juma'a.

Ya ce:

“Wannan labari ne mai daɗi kuma babban albishir ne a gare mu. Amma na yi magana da wasu mutane a INEC, kuma sun ce in jira zuwa gobe lokacin da za su fitar da sanarwarsu a hukumance.”

Mairiga ya bayyana fatan cewa INEC za ta tabbatar da rahotannin, ya ce to daga nan jam’iyyar za ta shiga harkokin yaƙin zaɓe.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Yau INEC za ta yi matsaya kan Pantami da wasu 'yan takara

Da zarar INEC ta sanar da amincewa da takarar Gwarzo a hukumance, NDC za ta maida hankali wajen ganin bayan Abba Kabir.

“Ina so in gode wa Allah na da ya ba ni wannan dama. Ina kuma godiya ga al’ummar Kano bisa damuwarsu kan wannan batu.
Dole ne mu ci gaba da yaƙin neman zaɓe da shiga gida-gida domin samun nasarar ɗan takararmu, in sha Allah.”

- Husseini Mairiga

Jam'iyyar NDC tana takara a Kano ko kuwa?

A halin yanzu babu abin da yake tabbatar da cewa an karbi korafin da jam’iyyar NDC ta shigar ganin an cire ‘dan takaranta a Kano.

Wani rahoto da Punch ta fitar ya ce INEC ba ta amince da takarar Aminu Abdussalam da Ladi Adebutu a Kanod a Ogun ba.

A Kano, an ce an yi watsi da korafin jam’iyyar adawa ta NDC ne saboda akwai karar da aka shigar a kotu, dole sai an gama shari’ar.

Idan labarin ya tabbata, sai alkali ya yi hukunci sannan INEC za ta san matakin da za ta dauka game da takaran gwamnan.

Kara karanta wannan

2027: Bayan gyare gyare INEC za ta fitar da sabon jerin 'yan takara

Tsohon mai daukar 'dan takaran NDC na Kano hoto, Hamza Ahmad Telan Mata ya sanar a Facebook cewa INEC ta karbi korafinsu.

APC ta ki yarda da batun canza 'dan takara

Alkali ya umarci hukumar zaɓe (INEC) ta canza ‘dan takaran Sanata a mazabar Imo ta yamma na jam'iyyar APC kamar yadda aka ji.

Rochas Okorocha, wanda ya mulki Imo daga shekarar 2011 zuwa 2019 ya karbo T a kotu bayan tsawon lokaci ana ta buga shari'a.

Jam’iyyar APC ba ta san ana yi ba, ta ce Gwamna Hope Uzodimma ne ɗan takararta a zaben baɗi domin Okrocha bai ci zaben gwani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng