Babban Zance: An ba Atiku Jakadan Tinubu Must Go na Najeriya
- Jagoran tafiyar Tinubu Must Go, Abba Hikima, ya kai wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ziyara, inda aka naɗa shi jakadan tafiyar
- Abba Hikima ya ceTinubu Must Go ta haɗa kai da kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku domin faɗaɗa tasirinsu a matakin unguwanni, ƙananan hukumomi da jihohi
- Manyan jiga-jigan siyasa, ciki har da Rotimi Amaechi, Austin Akobundu, Naja’atu Bala Muhammad da Dino Melaye, sun halarci taron haɗin gwiwar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jagoran ƙungiyar Tinubu Must Go (TMG), Abba Hikima, ya kai wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ziyara, inda aka naɗa Atiku a matsayin babban jakadan ƙungiyar.
Abba Hikima ne ya bayyana hakan bayan ziyarar, inda ya ce matakin wani muhimmin ci gaba ne a ƙoƙarin da suke yi na ceto Najeriya.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Abba Hikima ya ce ƙungiyar TMG ta kuma haɗa kai da kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku domin ƙarfafa haɗin gwiwarsu da masu goyon baya a faɗin ƙasar.
An naɗa Atiku Abubakar jakadan TMG
Abba Hikima ya bayyana cewa mambobin tafiyar Tinubu Must Go sun gana da Atiku, inda suka ba shi matsayin babban jakada.
Ya ce wannan mataki ya nuna haɗin kai tsakanin ƙungiyar da sauran masu fafutukar neman sauyi a Najeriya.
Jagoran tafiyar ya bayyana manufarsu a matsayin ƙoƙarin haɗa ƙarfi da faɗaɗa ayyukansu a dukkan sassan ƙasar, musamman a matakin tushe.
Manyan 'yan siyasa sun halarci taron
A cewar Abba Hikima, wasu manyan jiga-jigan 'yan siyasa da jami’an kwamitin yaƙin neman zaɓe sun halarci taron.
Daga cikinsu akwai tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi; Sanata Austin Akobundu, wanda aka bayyana a matsayin darakta-janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen; da Abdussamad Ibrahim Dasuki daga jihar Sokoto.

Kara karanta wannan
"Bai cancanta ba," An tono abin da zai iya zama matsala ga abokin takarar Atiku a 2027
Sauran sun haɗa da Hajiya Naja’atu Bala Muhammad, Sanata Dino Melaye da Salihu Tanko Yakasai, tare da wasu wakilai.
Ya ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen haɗa ayyukan ƙungiyar TMG da kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku domin ƙarfafa tsarin tattara magoya baya a matakin unguwanni, ƙananan hukumomi da jihohi.

Source: Facebook
Jagoran Tinubu Must Go ya bayyana cewa ƙungiyar za ta fara aiki tare kai tsaye da kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku.
Ya ce manufarsu ita ce gina haɗin gwiwar siyasa mai ƙarfi a faɗin Najeriya, inda za su haɗa magoya baya a matakin tushe.
ADC ta dage fara kamfen
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar ADC ta ɗage ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasarta a jihar Sokoto daga ranar Asabar, 31 ga Oktoba, zuwa Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026.
Wasu rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ta ce ta ɗauki matakin ne saboda buƙatun da suka shafi shiri da tsara yadda za a gudanar da taron.
ADC ta kuma zargi gwamnatin jihar Sokoto da hana wakilanta samun masauki a otal-otal gabanin taron, tare da zargin wasu magoya bayan jam’iyyar APC da makarkashiya.
Asali: Legit.ng
