An Barke da Murna a Gombe da INEC Ta Dawo da Pantami Takara

An Barke da Murna a Gombe da INEC Ta Dawo da Pantami Takara

  • Al’ummar Gombe sun fito kan tituna cikin dare domin murnar dawo da sunan Farfesa Isa Ali Pantami cikin jerin ’yan takarar gwamnan jihar na zaɓen 2027
  • Masu goyon bayan Pantami sun yi jerin gwanon motoci da babura a unguwannin Pantami, Jekadafari da sauransu yayin da matakin INEC ya tayar da muhawara
  • Wani mai goyon bayan ADC ya ce dawo da sunan Pantami na iya rage ƙuri’un APC da PDP, yayin da wani mai goyon bayan APC ya soki masu jiran a hana malamin takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Al’ummar jihar Gombe sun fito cikin daren nan suna murna bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta dawo da sunan Farfesa Isa Ali Pantami cikin jerin ’yan takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Yau INEC za ta yi matsaya kan Pantami da wasu 'yan takara

Mutane da dama sun yi jerin gwanon motoci da babura a kan titunan jihar domin nuna farin cikinsu da matakin da hukumar zaɓen ta ɗauka.

Sheikh Isa Ali Pantami
Masu murnar dawowar Pantami takara a jihar Gombe da dantakarar a gefen dama. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Legit Hausa ta tabbatar da cewa masu murnar sun zagaya unguwanni daban-daban na cikin birnin Gombe, musamman manyan tituna, inda wasu suka fito da motocin siyasa masu ɗauke da hotunan Pantami.

Jama’a sun yi murna a titunan Gombe

Legit ta zagaya jihar Gombe da dare inda ta ga masu murnar a unguwannin Pantami, Jekadafari, Bolari da Tudun Wada, da sauran sassan birnin Gombe.

Wasu sun yi amfani da motocin siyasa wajen gudanar da jerin gwanon, yayin da wasu suka fito da babura domin nuna goyon bayansu ga tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani.

Dawo da sunan Pantami cikin jerin ’yan takarar ya zama babban abin tattaunawa a jihar, inda magoya bayansa da sauran masu bibiyar siyasa suka bayyana ra’ayoyinsu kan matakin INEC.

Haka kuma, batun Pantami ya zama sabuwar tattaunawa a wuraren zaman jama’a a cikin birnin Gombe.

Wani mai goyon bayan ɗan takarar gwamnan ADC a jihar, Muhammad Sa’idu, ya bayyana farin cikinsa da dawo da sunan malamin cikin jerin ’yan takarar.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: 'Yan bindiga sun nuna wa mata kusan 30 da karamin yaro rashin imani

Ya ce:

“Ko ba komai, mu ’yan adawa mun yi farin ciki. Hakan zai ƙara raunana APC a Gombe. Mu dai damuwarmu ita ce APC ta samu ƙuri’u kaɗan, PDP ma haka, mu kuma mu kwashe mafi yawan ƙuri’u domin mu yi nasara.”

Dan APC ya yi korafi.

A kafafen sada zumunta ma, batun dawo da sunan Pantami ya jawo muhawara sosai, inda wasu suka bayyana ra’ayoyinsu kan yadda jam’iyyar APC za ta tunkari zaɓen gwamnan jihar.

Haji Shehu, wanda ke wallafa rahotanni da sharhi kan gwamnan jihar Gombe, ya soki ’yan APC da yake ganin suna jiran a hana Pantami takara maimakon su mayar da hankali kan tallata ɗan takararsu.

A cikin saƙon da ya wallafa a Facebook, ya ce:

“Gaskiya mai ɗaci ga jam’iyyar APC. Wallahi abin kunya ne a ce ɗan APC yana jiran kotu ko INEC ta dakatar da Pantami daga takara.
“Wallahi, ba da wannan shifcin gizon muka kafa jam’iyyar APC ba. Shiga muka yi lungu da saƙo muka nemi jama’a, kuma muka yi nasara da yardar Allah.

Kara karanta wannan

An farmaki yan APC yayin da Gwamna Radda ya kaddamar da kamfen a Katsina

“Amma saboda lalacewa, wai yanzu ɗan APC ne yake jiran a hana Pantami takara saboda ya ci banza a zaɓe! Haba jama’a, mu gaya wa kanmu gaskiya mana!
“Jam’iyyar APC ta yi aiki a jihar Gombe. Me ya sa ’ya’yan jam’iyyar ba za su iya yaƙin neman zaɓe da irin ci gaban da ta kawo ba?
“Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Gombe sanannen mutum ne, fitacce a harkar siyasa, kuma babu inda za ka je ka sha wahalar tallata shi.
“Akwai buƙatar waɗanda aka ɗaura wa nauyin tallata ’yan takarar jam’iyyar APC su fito su tallata wannan tafiya da gaske, kamar yadda muka yi a baya ta kafafen intanet da wajen intanet lokacin da muka kafa gwamnati.
“Amma abin kunya ne, wallahi, a ce sabon yanka a siyasa irin Pantami, shi ake tsoro.”
Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami yana yi wa jama'a bayani a wajen taro. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

An rusa takarar Uzodimma

A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke fitowar Gwamna Hope Uzodinma a matsayin ɗan takarar APC na kujerar sanatan Imo ta Yamma.

Mai shari’a Obiora Egwuatu ya ce hujjojin da aka gabatar wa kotun sun nuna cewa Uzodinma bai lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar da aka gudanar a yankin sanatan ranar 18 ga Mayu ba.

Kotun ta bayyana cewa tsohon gwamnan jihar, Sanata Rochas Okorocha, ne ya samu mafi yawan ƙuri’u a zaɓen fidda gwanin, don haka ta umarci INEC ta amince da shi a matsayin ɗan takarar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng