Netanyahu Ya Samu Matsala a Zaben Israila, an Ji Halin da Kujerarsa Ke ciki
- Hasashe ya nuna cewa hadakar da ke goyon bayan Netanyahu za su samu kujeru 53 cikin 120, yayin da ƙungiyar adawa za ta samu 48
- Jam’iyyun da ke wakiltar Larabawa ‘yan Isra’ila na iya samun kujeru 19, lamarin da ya sa Gadi Eisenkot zai buƙaci goyon bayansu domin samun damar kafa gwamnati
- Netanyahu ya yi kira da a kafa gwamnati mai ƙarfi ta hannun masu ra’ayin rikau, tare da bayyana yiwuwar sake kai hare-haren soja kan Iran tare da Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Israila - Benjamin Netanyahu na iya ci gaba da zama firaministan riƙon ƙwarya na Isra’ila bayan goyon bayan da ya samu daga masu zaɓe Yahudawa ya rage damar da abokan hamayyarsa ke da ita ta kawar da shi daga mulki.
Hakan na zuwa ne duk da cewa hadakar jam’iyyun da ke goyon bayan Netanyahu sun rasa rinjayen kujeru a majalisar dokokin ƙasar, wato Knesset.

Source: Getty Images
Me hasashen sakamakon zaɓen ya nuna
Tashar Arab News ta ce a ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, bayan an ƙirga kusan kashi 86 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, manyan tashoshin talabijin uku na Isra’ila sun yi hasashen cewa hadakar jam’iyyun masu ra’ayin rikau, masu tsattsauran ra’ayin da kuma Yahudawan Orthodox za ta samu kujeru 53 cikin 120.
A gefe guda, ƙungiyar adawa ƙarƙashin jagorancin Gadi Eisenkot na iya samun kujeru 48.
Jam’iyyun da ke wakiltar Larabawa ‘yan Isra’ila kuma ana hasashen za su samu kujeru 19, adadin da ba a taɓa ganin irinsa ba a irin wannan hasashe.
Wannan sakamako na iya zama cikas ga Eisenkot, domin zai buƙaci gagarumin goyon bayan waɗannan jam’iyyu domin samun damar kafa gwamnati.
Sakamakon na iya sauyawa yayin da ake ci gaba da ƙirga ƙuri’u. Duk da haka, hadakar jam’iyyun da ke adawa da Netanyahu, ba ta kai matsayin da wasu hasashen zaɓe na kafin ranar kaɗa ƙuri’a suka nuna ba.
Netanyahu zai ci gaba da riƙe mulki
Ana sa ran Netanyahu zai ci gaba da zama firaministan riƙon ƙwarya yayin da ake tattaunawar haɗa kawancen jam’iyyun domin kafa gwamnati.
Mai yiyuwa ne ya ci gaba da riƙe matsayin har zuwa wani sabon zaɓe a shekara mai zuwa idan jam’iyyun siyasa suka kasa cimma matsaya.
Guy Lurie, wani mai bincike a Cibiyar Dimokuraɗiyya ta Isra’ila, ya ce gwamnatin riƙon ƙwarya tana da irin ikon da gwamnati ta yau da kullum take da shi a hukumance.
Sai dai ya bayyana cewa ana sa ran irin wannan gwamnati ta yi taka-tsantsan wajen amfani da ikonta, kuma tana da ƙarancin ’yancin yanke wasu shawarwari.
Duk da waɗannan ƙuntatawa, masana sun ce gwamnatin riƙon ƙwarya na iya ci gaba da ɗaukar muhimman matakai, ciki har da waɗanda suka shafi yaƙin da ake yi da Iran.
Netanyahu ya yi maganar sake kai hari Iran
Netanyahu ya yi jawabi ga magoya bayan jam’iyyarsa ta Likud bayan ƙarfe 3:00 na dare, inda ya yi kira da a kafa gwamnati mai ƙarfi ta ƙasa.

Kara karanta wannan
Farfesa ya kunyata NDC ta su Kwankwaso da Obi bayan ganin sunansa a kwamitin kamfe
Ya kuma jaddada nasarorin sojojin Isra’ila, tare da bayyana yiwuwar sake gudanar da ayyukan soja tare da Amurka domin kai wa Iran hari.
Netanyahu, wanda ke da alaƙa ta siyasa da Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce ƙasashen biyu suna da wata dama ta musamman a tarihi ta kawar da abin da ya kira barazanar Iran har abada.
Trump ya taɓa kira ga masu zaɓe a Isra’ila da su ci gaba da goyon bayan Netanyahu domin su kammala abin da suka fara a Iran.

Source: Twitter
Netanyahu ya yi zarge-zarge
A wani labarin kuma, kun ji cewa firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi zargin an samu kura-kurai bayan kawancensa ya rasa rinjayen kujeru a Knesset.
Netanyahu ya zargi jam'iyyun siyasar Larabawa da magudin zabe bayan sakamakon farko ya nuna cewa kawancen siyasarsa bai samu rinjayen kujeru ba.
Asali: Legit.ng

