An Yi wa Kwankwaso ba Dadi da Ya Shiga Gombe, Ya Soki Gwamnatin Jihar
- Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin jihar Gombe da matsa wa masu wani wurin taro lamba, lamarin da ya tilasta sauya wajen gudanar da taro
- Kwankwaso, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, ya jagoranci taron tattaunawa da al’ummar Gombe ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026
- Jagoran Kwankwasiyya ya kuma gana da ’yan takarar jam’iyyar a jihar, tare da karɓar ziyarar dattawan ƙungiyar ci gaban Yamaltu Deba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin jihar Gombe da kawo cikas ga shirinsa na gudanar da taron jam’iyyar a jihar.
Kwankwaso ya ce an tilasta sauya wurin taron babu shiri bayan da ake zargin gwamnatin jihar ta matsa wa masu wurin taron lamba.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Rabiu Kwankwaso ya yi ne a wani sako da hadimin sa, Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Yadda aka sauya wurin taron NDC
An shirya gudanar da taron tattaunawar al’umma na NDC ne a wajen taron Linmana da ke gaban gidan mai na Ummodah a unguwar Tumfure, Gombe.
Sai dai a cikin sanarwar da aka wallafa kan ziyarar Kwankwaso, an bayyana cewa masu wurin sun fuskanci matsin lamba daga gwamnatin jihar, wanda ya tilasta sauya wurin taron duk da ƙarancin lokacin da ya rage.
Ba a bayyana sunan wani jami’in gwamnati da ake zargi da matsa wa masu wurin lamba ba, kuma ba a samu martanin gwamnatin Gombe kan zargin ba.

Source: Facebook
Abubuwan da aka tattauna a taron
A yayin taron da aka gudanar ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026, Kwankwaso ya yi magana kan manyan ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta tare da bayyana hanyoyin da za a bi wajen magance su.
Jagoran NDC a Najeriya ya kuma miƙa takardun shaidar cin zaɓe ga wasu ’yan takarar jam'iyyar da ba su karɓi nasu ba.
Bayan haka, tsohon gwamnan ya gana da ’yan takarar jam’iyyar a jihar domin tattauna harkokin jam’iyya, haɗin kai da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027.
A wani ɓangare na ziyararsa, Kwankwaso ya karɓi ziyarar goyon baya daga dattawan ƙungiyar ci gaban karamar hukumar Yamaltu Deba.
Tawagar ta samu jagorancin Musa Dalla, ɗan takarar NDC mai neman kujerar wakiltar mazabar tarayya ta Yamaltu/Deba.
Jam'iyyar NDC ta soki Gwamnatin Kano
A wani labarin, mun rahoto cewa ƙungiyar Kwankwasiyya ta zargi gwamnatin jihar Kano da siyasantar da zargin harin da aka kai wa ayarin motocin jagoranta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ƙungiyar ta bayyana cewa jihar Kano mallakin dukkan mazaunanta ce, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da suke goyon baya ba, don haka gwamnati na da alhakin kare rayuka da haƙƙoƙin kowane ɗan ƙasa.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Dr Habibu Sale Mohammed, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya mayar da martani kan harin da aka ce an kai wa ayarin Kwankwaso.
Asali: Legit.ng

