Shirin Kifar da Tinubu Ya Kankama, Ana Daf da Fitar da Dan Takara 1 na Adawa
- Lawal Daura na jam’iyyar APM ya ce tattaunawar haɗakar ’yan adawa domin samar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a 2027 na tafe
- Daura ya bayyana cewa ana tattaunawa tsakanin masu neman takara, jam’iyyun siyasa da manyan masu ruwa da tsaki
- Ya zargi gwamnati da rashin bayyana hujjojin ƙididdigar tattalin arziki, yana zargin cewa an biya mutane domin zuwa taron Tinubu a Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), Lawal Daura, ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu.
Daura ya ce an gaggauta tattaunawar haɗakar ’yan adawa da nufin samar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027, yana mai cewa nan ba da jimawa ba ’yan Najeriya za su san matsayar haɗakar.

Source: Facebook
Shirin yan adawa kan Bola Tinubu
Da yake magana a wata hira da Arise News ranar Litinin, Daura ya ce haɗakar ta amince da tsarin tattaunawa a matakai uku.
Matakan sun ƙunshi masu neman takarar shugaban ƙasa, jam’iyyun siyasa da manyan masu ruwa da tsaki, domin cimma matsaya kan ɗan takara guda.
Daura ya ce sun rarraba tattaunawa tsakanin masu neman takara, jam’iyyun siyasa da manyan masu ruwa da tsaki domin hanzarta cimma matsaya, duk da jinkirin da ya samu sakamakon burin wasu ’yan siyasa na neman takara.
Ya ce:
“Abin takaici, dagewar wasu ’yan takara kan dalilan da ya sa ya kamata a ba su dama ko a yi la’akari da su ya jinkirta tattaunawar sosai, amma a baya-bayan nan, an gaggauta tattaunawar, kuma ina ganin nan ba da jimawa ba ’yan Najeriya za su san matsayarmu.
"Na tabbata wannan matsaya za ta kasance mai kyau, domin mun yi imanin cewa haɗuwa da mara wa mutum guda baya ne zai sauƙaƙa wa ’yan adawa ƙwace mulki."

Source: Facebook
An zargi gwamnatin Tinubu da karairayi
Da yake magana kan ikirarin gwamnatin tarayya game da bunƙasar tattalin arziki, Lawal Daura ya ce ƙididdigar ba ta da wani amfani idan har ’yan Najeriya ba su ga sauyi mai kyau a rayuwarsu ba.
Ya ce:
“Na yarda, ko kuma mu ce mun amince, cewa idan ’yan Najeriya ba su ji amfanin waɗannan ikirari ba, to ko dai ba daidai ba ne ko kuma an yi ƙarya da gangan. Da a ce gaskiya ne, da ’yan Najeriya sun ji amfaninsa kuma sun gani a rayuwarsu.
“Da ba za a ga damuwa, ƙunci da takaici a fuskokin mutane ba. Wannan shi ne matsayarmu. Na biyu, batun alkaluman GDP ko bunƙasar tattalin arziki ya yi kama da ba da labari kawai. Wane irin sauyi ne za a iya gani a zahiri da ya tabbatar da waɗannan ikirari?”
Dangane da zargin cewa kowace jiha na bin ta bashin naira biliyan 250 daga kuɗaɗen NLNG, Daura ya ce alkaluman sun fito ne daga rahoton binciken kuɗi da fadar shugaban ƙasa da gwamnonin jihohi suka amince da shi. Ya ƙalubalanci gwamnatin tarayya da ta bayyana yadda ta yi lissafinta.
Na kusa da Atiku ya kawo mafita
An ji cewa Kenneth Okonkwo ya bayyana hanyar da 'yan adawa za su iya kalubalantar jam'iyyar APC a zaben 2027.
Okonkwo ya danganta hujjarsa da zaɓen 2023, lokacin da kuri’un Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suka rabu.
Tsohon jigo a yaƙin neman zaɓen Peter Obi ya ce rashin haɗin kan adawa na iya sake raba kuri’u a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng


