Rana ba Ta Karya: Yau INEC za Ta Yi Matsaya kan Pantami da Wasu 'Yan Takara

Rana ba Ta Karya: Yau INEC za Ta Yi Matsaya kan Pantami da Wasu 'Yan Takara

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, ta ce za ta tattauna kan makomar Sheikh Isa Ali Pantami, Ladi Adebutu da sauran ’yan siyasar da ta cire sunayensu
  • INEC ta cire sunayen Pantami na PDP a Gombe da Adebutu na PDP a Ogun, tare da Aminu Gwarzo na NDC a Kano da wasu ’yan takara a wasu jihohi
  • ’Yan siyasar da abin ya shafa da jam’iyyunsu sun nuna rashin amincewa da matakin, suna mai cewa sun cika sharudan da doka ta tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar INEC ta ce za ta yanke matsaya kan makomar Sheikh Isa Ali Pantami, Ladi Adebutu da sauran ’yan siyasar da aka cire sunayensu daga jerin ƙarshe na ’yan takarar gwamna a zaɓen ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

Kara karanta wannan

APC na tsaka mai wuya, ana neman cire sunan ɗan takararta na gwamna a zaɓen 2027

Kwamishinan INEC na ƙasa, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi ranar Laraba.

Shugaban hukumar INEC
Shuaban INEC, Farfesa Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Haruna ya shaidawa jaridar Punch cewa hukumar za ta tattauna kan jerin ’yan takarar a taronta na gaba da aka shirya gudanarwa a yau Alhamis.

INEC za ta duba batun 'yan takara

Pantami na neman kujerar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, yayin da Adebutu ke neman kujerar gwamnan Ogun a ƙarƙashin jam’iyyar ta PDP.

Hukumar INEC ta cire sunayensu daga jerin ƙarshe da ta wallafa ranar 10 ga Oktoba, tare da na Aminu Gwarzo, ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, da Danjuma Laah, ɗan takarar gwamnan Kaduna na NDC.

Haka kuma, hukumar ta cire sunayen ’yan takarar gwamna na jam’iyyun SDP, NNPP, AAA a jihar Bauchi.

’Yan takarar da abin ya shafa a Bauchi su ne Abdullahi Yakubu, Musa Zubairu, Ahmed Shuaibu da Mohammed Aminu.

Wannan mataki ya jawo zanga-zanga da ɗaukar matakan shari’a daga wasu ’yan takarar da jam’iyyunsu, waɗanda ke neman INEC ta sake duba matsayarta.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Kotu ta bukaci INEC ta sauya yan takara

Haruna ya ce:

“Game da jerin ƙarshe na ’yan takara, za mu tattauna a kai a taron hukumar na gaba ranar Alhamis.”
Sheikh Pantami da Aminu Gwarzo
Sheikh Isa Ali Pantami da Aminu Gwarzo. Hoto: Abba Sani Pantami|Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Dalilin cire sunayen ’yan takara

INEC ta danganta cire sunayen ’yan takarar da gazawar jam’iyyunsu wajen gabatar da rajistar mambobinsu a lokacin da doka ta tanada.

Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumba, 2026, wanda ya tabbatar da ingancin sashe na 77(5), 77(6) da 77(7) na Dokar Zaɓe ta 2026.

Waɗannan tanade-tanade sun buƙaci jam’iyyun siyasa su miƙa rajistar mambobinsu ga INEC kafin gudanar da sahihan zaɓukan fitar da gwani, tarukan jam’iyya da manyan tarukan zaɓen shugabanni.

Hukumar ta ce Kotun Ƙoli ta kuma tabbatar da ingancin jadawalin da ta fitar, wanda ya buƙaci jam’iyyun su gabatar da rajistar mambobinsu tsakanin 21 ga Afrilu da 10 ga Mayu, 2026.

A cewar INEC, jam’iyyun da ba su cika wannan sharadi ba ba su cancanci tsayar da ’yan takara a zaɓen ba.

Kara karanta wannan

2027: Bayan gyare gyare INEC za ta fitar da sabon jerin 'yan takara

Za a mayar da sunan dan takara

A wani labari, mun ruwaito cewa wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta soke wallafa sunan Ibrahim Lukman a matsayin ɗan takarar jam’iyyar NDC na mazaɓar tarayya ta Oshodi/Isolo I a zaɓen 2027.

Mai shari’a Akintayo Aluko ne ya yanke hukuncin ranar 20 ga Oktoba, inda ya bayyana cewa Lukman bai shiga zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ba.

Kotun ta ce INEC ta saɓa wa Dokar Zaɓe ta 2026 duk da cewa jami’anta sun sanya ido kan zaɓen fidda gwani na ranar 29 ga Mayu, wanda Olumuyiwa Owadara ya yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng