An Gwabza Rikici tsakanin Sojoji da Jama'a a Lawanti da ke Gombe
- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya mika sakon ta’aziyya ga al’ummar Lawanti da iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a wani lamari tsakanin jami’an sojoji da mazauna yankin
- Pantami ya bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa su kwantar da hankalinsu, su guji daukar matakan da za su iya kara dagula lamarin
- Tsohon ministan ya kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar abin da ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya mika sakon ta’aziyya ga al’ummar Lawanti da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe, kan wani lamari da ya faru tsakanin jami’an sojoji da mazauna yankin.
Pantami ya bayyana hakan ne a cikin sakon ta’aziyya mai dauke da kwanan wata 21 ga Nuwamba, 2026, inda ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a X, Pantami ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da al’ummar yankin ke bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali, yana mai bayyana alhini kan asarar rayuka da firgicin da abin ya jawo.
Pantami ya yi addu’a ga mamata
A cikin sakon, Pantami ya ce shi da iyalansa suna mika ta’aziyyarsu ga dukkan iyalan da suka rasa ’yan uwansu, tare da jajanta wa wadanda suka samu raunuka da sauran mutanen da lamarin ya shafa.
Ya bayyana cewa Lawanti ta shahara wajen zaman lafiya, karbar baki da mutunta hukumomi, don haka abin takaici ne yadda irin wannan lamari ya faru a yankin.
Tsohon ministan ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa wadanda suka rasu, ya sanya su a Aljannatul Firdaus, ya kuma ba iyalansu hakurin jure wannan rashi.
Ya kuma roki Allah ya ba wadanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa tare da dawo da zaman lafiya a Lawanti da dukkan karamar hukumar Akko.
Ya bukaci a gudanar da bincike
Pantami ya yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su kwantar da hankulansu, su rungumi zaman lafiya, tare da guje wa daukar matakan da ka iya kara ruruta rikicin.
Ya kuma bukaci hukumomin da suka dace su gudanar da cikakken bincike ba tare da nuna son kai ba domin gano hakikanin abin da ya faru.

Source: Original
A cewarsa, binciken zai taimaka wajen gano gaskiya, hana sake faruwar irin wannan lamari da kuma tabbatar da adalci da zaman lafiya mai dorewa.
'Yan APC sun yi hadari a Gombe
A wani labarin, mun rahoto cewa kungiyar Pantamiyya Movement ta yi ta’aziyya ga iyalan mutanen da hatsarin mota ya rutsa da su a hanyar Deba zuwa Talasse a jihar Gombe.
Hatsarin ya rutsa da shugaban APC na jihar, Mohammed Dantata Ndus, da daraktan yakin neman zaben jam’iyyar na 2027, Sa’adu Hassan.
Kungiyar ta yi addu’ar Allah ya jikansa da mai babur da ya rasu a hatsarin, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Asali: Legit.ng

