Jam'iyyar NDC Ta Yi Barazana ga INEC kan Cire Sunan Aminu Gwarzo daga Takara a Kano
- NDC a Kano ta ce za ta dauki mataki kan INEC idan hukumar ta gaza warware korafinta kan cire sunan Aminu Abdussalam Gwarzo daga jerin ’yan takarar gwamna
- Shugaban jam’iyyar na jihar, Husseini Mairiga, ya ce har yanzu ba su samu amsa daga INEC ba duk da cikar wa’adin korafi na ranar 24 ga Oktoba
- Mairiga ya dage cewa Gwarzo ya cancanci tsayawa takara kuma cikakken ɗan jam’iyyar ne da aka yi wa rajista
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a Jihar Kano ta yi barazanar maka Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a kotu.
NDC ta yi barazanar kai karar INEC ne kan cire sunan ɗan takararta na gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, daga jerin sunayen ’yan takarar zaɓen gwamnan jihar na 2027.

Source: Facebook
Shugaban NDC na jihar, Husseini Mairiga, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar Leadership ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoban 2026.
Husseini Mairiga ya ce jam’iyyar za ta nemi haƙƙinta ta hanyar shari’a idan INEC ta gaza warware korafin da ta shigar kan wannan lamari.
Ya ce har yanzu jam’iyyar ba ta samu wani martani daga hukumar ba, duk da cikar wa’adin da aka bayar na shigar da korafe-korafe a ranar 24 ga Oktoban 2026.
NDC ta ce ba ta samu amsa daga INEC ba
Mairiga ya ce har yanzu babu wani bayani da suka samu daga INEC kan korafin da suka shigar.
“Har zuwa yanzu, ba mu ji komai daga INEC ba. Na tambayi shugabanninmu na ƙasa ma, amma su ma ba su samu wani bayani ba,” in ji shi.
Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa yana shirin zuwa Abuja ranar Litinin, inda zai nemi sanin halin da korafin jam’iyyar yake ciki da kuma matakin da ya kamata su ɗauka na gaba.
Ya ce zai yi amfani da ziyarar wajen neman ƙarin bayani daga masu ruwa da tsaki kan lamarin.
Jam’iyyar ta shirya zuwa kotu
Mairiga ya jaddada cewa NDC ba za ta zuba ido ta bar batun ya tafi haka nan ba idan INEC ta gaza ba ta amsa kan korafinta.
“Idan INEC ba ta ba mu wani bayani ba, za mu tafi kotu. Ba za mu iya barin lamarin haka kawai ba,” in ji shi.
A baya dai, NDC ta shigar da korafi ta hannun shugabanninta na ƙasa, bayan INEC ta umarci jam’iyyun siyasa da abin ya shafa su gabatar da koke-kokensu kan cire sunayen ’yan takararsu daga jerin waɗanda za su fafata a zaɓen 2027 kafin ranar 24 ga Oktoba.
Sai dai, a cewar Mairiga, har yanzu ba su samu amsar da suke jira daga hukumar zaɓen ba.
NDC ta dage cewa Gwarzo ya cancanci takara
Shugaban jam’iyyar na Kano ya kuma bayyana cewa Aminu Abdussalam Gwarzo ya cika sharuddan tsayawa takarar gwamna, yana mai cewa ɗan jam’iyyar ne da aka yi wa rajista yadda ya kamata.
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara matsowa, batun cire sunayen ’yan takara daga jerin sunayen INEC na ci gaba da zama abin da wasu jam’iyyun siyasa ke ƙalubalanta.

Source: Original
OK Movement ta yi korafi kan kwamitin NDC
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Obi-Kwankwaso Movement ta soki jam’iyyar NDC kan sanar da sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓenta na kasa.
Ƙungiyar ta kuma yi ikirarin cewa tana da ingantaccen tsarin siyasa a matakin ƙasa wanda ya fi na wasu masu fafutukar neman mulki ƙarfi.
Asali: Legit.ng


