Babban Labari: INEC Ta Amince da Sheikh Pantami a Matsayin Dan Takarar Gwamna a Gombe
- INEC ta amince da tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, a matsayin dan takarar gwamnan jihar Gombe karkashin jam'iyyar PDP
- Haka zalika, hukumar ta amince ɗan takarar gwamnan Kano na NDC, Abdulsalam Gwarzo, ya shiga babban zaɓen 2027
- Hukumar ta ƙi amincewa da ƙorafin ɗan takarar gwamnan Ogun na PDP, Ladi Adebutu, wanda ya nemi a sake duba cire sunansa daga jerin ’yan takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a matsayin ɗan takarar gwamnan PDP a jihar Gombe.
Haka zalika, INEC ta sahalewa dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar NDC, Kwamared Abdulsalam Gwarzo, ya fafata a babban zaben gwamnoni da za a gudanar a watan Fabrairun 2027.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar ta bayyana cewa amincewa da yan takarar biyu tana ƙarƙashin hukuncin da kotu za ta yanke kan shari’o’in da ke gudana a gabanta.
INEC ta samu korafe-korafe 69
Wata majiya a INEC ta ce hukumar ta samu ƙorafe-ƙorafe 69 daga jam’iyyun siyasa kan cire ko rashin sanya sunayen wasu ’yan takara a jerin masu neman kujerun gwamna da na majalisun dokokin jihohi.
“Mun samu ƙorafe-ƙorafe 69 daga jam’iyyun siyasa. Wasu sun yi nasara, ina ganin kusan 36, sauran kuma ba su yi nasara ba,” in ji majiyar.
Sai dai majiyar ta bayyana cewa hukumar na jiran cikakken adadin ƙorafe-ƙorafen da suka yi nasara daga sashen shari’arta, wanda ke shirya sanarwar da za a fitar kan hukuncin da aka yanke.
Matsayar INEC kan Pantami da Gwarzo
Dangane da Pantami da Gwarzo, majiyar ta ce hukumar INEC ba ta da wata matsala da tsayawarsu takara, amma shari’o’in da ke gaban kotu na iya shafar cancantarsu.
“Eh, an amince da Pantami,” in ji majiyar yayin da aka tambaye ta game da ɗan takarar gwamnan PDP a jihar Gombe.
Game da Gwarzo kuwa, majiyar ta ce amincewar da aka ba shi tana ƙarƙashin hukuncin ƙarshe da kotu za ta yanke kan shari’ar da ta shafi takararsa.
“Saboda akwai shari’a a kotu, kotu na iya yanke hukunci daban, Don haka, amincewarsa tana ƙarƙashin duk hukuncin ƙarshe da kotu za ta yanke,” in ji majiyar.
Majiyar ta kuma tabbatar da cewa ƙorafin LadinAdebutu, dan takarar gwamnan PDP a jihar Ogun bai yi nasara ba.
Matakan sun biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da ’yan takara da jam’iyyun siyasa suka shigar bayan INEC ta kasa sanya sunayensu cikin jerin da ta wallafa gabanin babban zaɓen 2027.
Pantami da Gwarzo na daga cikin fitattun ’yan takarar gwamna waɗanda sunayensu ba su bayyana a jerin da hukumar INEC 1ta fitar a watan Oktoba ba.
Ana sa ran INEC za ta fitar da sanarwa a hukumance kan sakamakon bitar ƙorafe-ƙorafen.
Asali: Legit.ng

