Kotu Ta Karbe Takarar Gwamna Uzodinma amma Jam’iyyar APC Ta Yi Mursisi

Kotu Ta Karbe Takarar Gwamna Uzodinma amma Jam’iyyar APC Ta Yi Mursisi

  • APC a jihar Imo ta ce Gwamna Hope Uzodimma ne har yanzu ɗan takararta na kujerar sanatan Imo ta Yamma
  • A zaɓen 2027, jam’iyya mai mulki ta nuna ba ta san da batun takarar Rochas Okorocha ba, ba shi ne ya ci zabe ba
  • Duk da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta amince da nasarar Rochas Okorocha, ba a so a sauya Uzodinma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Imo - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Imo ta dage Gwamna Hope Uzodimma bai rasa takararsa ga Rochas Okorocha ba.

APC ta ce gwamnan shi ne ne ɗan takararta na kujerar sanatan yankin Imo ta Yamma a zaɓen 2027, duk da hukuncin kotu.

Gwamnan Imo
Gwamnan Imo wajen taron magoya bayan Bola Tinubu Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

APC ta ki karbar rushe takarar Hope Uzodinma

The Cable ta ce jam’iyyar ta bayyana matsayin ta ne ta hannun Kakakin APC na Imo a wani jawabi da ya fitar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

2027: Kotu ta rusa takarar shugaban gwamnonin APC na Najeriya

A cikin wata sanarwa da Jones Onwuasoanya ya fitar, ya ce jam’iyyar ta ce babu wani sauyi a matsayinta game da takara.

Jam’iyyar ta ce Hope Uzodimma ne ya lashe zaɓen fitar da gwani, ya samu gagarumin goyon bayan mafi yawan ‘ya ‘yanta.

Wannan mataki zai kawo wa takarar Rochas Okorocha tangarda shi da yake son ya sake koma wa majalisar dattawa.

Jawabin kakakin jam'iyyar APC a Imo

Sanarwar ta ce:

“Ba tare da wani ruɗani ba, jam’iyyar APC na son bayyana cewa Mai Girma Sanata Hope Uzodimma, CON, har yanzu shi ne ɗan takararmu na kujerar Sanatan Imo ta Yamma, kasancewar ya lashe zaɓen tsaida gwani tare da gagarumin goyon bayan mafi yawan mambobin jam’iyyarmu.”

Jam’iyyar APC ta ƙara da cewa lauyoyinta za su nazarci hukuncin kotun kan batun, sannan sai su ɗauki matakin da ya dace.

Daily Post ta rahoto cewa jam’iyyar ta kuma buƙaci mambobinta da magoya bayanta su ci gaba da ƙoƙarin ganin an lashe zabe.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Yau INEC za ta yi matsaya kan Pantami da wasu 'yan takara

Ta nemi kar su bari wani abu ya ɗauke musu hankali ba, wajen ƙoƙarin ganin APC ta yi nasara a dukkan mazaɓun da ke jihar Imo.

Alƙali Obiora Egwuatu ya yi hukunci cewa INEC ta karbe tikiti, ta ba wa tsohon gwamnan Imo, Sanata Rochas Okorocha.

Kotu ta gamsu cewa mafi yawan 'yan jam'iyyya shi su ka zaba ya nemi kujerar sanata a takarar 2027.

APC ba ta yi la’akari da hukuncin Egwuatu ba, ta ce ba Okorocha ba ne ya yi nasara a zaben tsaida ‘dan takaran sanata.

Tinubu a Imo
'Yan kungiyar magoya bayan Bola Tinubu a Imo Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

'Dan takaran NDC ya yi wa jam'iyya tsiya

Saura kwanaki a shiga zaben 2027 sai aka ji labari Joseph Danjuma ya yi wa NDC bore alhali an dogara da shi wajen kamfe.

Sakataren yada labaran jam’iyyar NDC na Nasarawa ya canza gida, yana tare da ‘dan takaran gwamna na SDP a zaben badi.

Tsohon kakakin jam’iyyar hamayyar yana ganin babu laifi mutum ya raba kafa a siyasa, ya yi koyi da su Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng