Wike Ya Yi Hadin Gambiza daga Jam’iyyu, Ya Tsaida ‘Yan Takaran da Za Su Zaba a 2027
- Rainbow Coalition ta su Nyesom Wike ta saki sunayen ’yan takarar da take goyon baya a zaɓen shekarar 2027
- Jam’iyyar APC mai mulki ta samu mafi yawan kujerun Majalisar Wakilai da na Dokokin jihar Rivers a kan PDP
- Gamayyar gambizar na shirin haɗa kan ’yan siyasa domin tallafa wa Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Rivers - Gamayyar Rainbow Coalition da Nyesom Wike yake jagoranta, ta bayyana ’yan takarar da take goyon baya.
Gamayyar ta zaɓo ’yan takarar ne daga jam’iyyun APC da PDP, ta ce su za ta mara wa baya a zaɓen 2027 a jihar Rivers.

Source: Facebook
'Yan takaran Rainbow coalition a jihar Rivers
An ga cikakken jerin ’yan takarar na zaben 2027 da babban hadimin Wike, wato Olayinka Lere ya wallafa sunayensu a kafar X.
An bayyana sunayen ’yan takarar a wani taro da aka yi a filin wasa na Yakubu Gowon da ke Fatakwal, ranar 27 ga Oktoba 2026.
Wannan gamayya tana neman haɗa kan ’yan siyasa daga jam’iyyun biyu domin taimaka wa Shugaba Bola Tinubu ya zarce.
Ko da duk sun yi tarayya a kan zaben Tinubu, ’yan takarar za su fafata a sauran kujeru ƙarƙashin jam’iyyun da suke ciki.
APC za su bi a zaben gwamnan Rivers
A zaben gwamnan Rivers kuma, za a bi tikitin jam’iyyar APC ne domin ganin Kingsley Chinda ya gaji Gwamna Simi Fubara.
Idan an tashi zaben majalisar dattawa, ‘yan hadin gambizar sun bar wa jam’iyyar PDP kujerar Sanatan Rivers ta Kudu.
Haka zalika jam’iyyar adawa ta samu ‘yan takara uku a zaben 'yan majalisar wakilai na tarayya.
Inda aka fi waiwayar jam’iyyar PDP shi ne a zaben ‘yan majalisar dokokin jihar Rivers da za a goyi bayan ‘yan takaranta 10.

Kara karanta wannan
‘Dan majalisar Kano ya tuno alherin da Tinubu ya yi wa Buhari a kokarin tallar APC
Yadda Rainbow Coalition ta yi rabon takara
1. ’Yan takarar gwamna
Muƙami | Sunan ɗan takara | Jam’iyya |
Gwamna | Kingsley Ogundu Chinda | APC |
Mataimakin gwamna | Major Jack | APC |
2. ’Yan takarar sanata
Yankin sanata | Sunan ɗan takara | Jam’iyya |
Rivers West | Felix Amaechi Obua | APC |
Rivers East | Onyesom Allwell Iheacho | APC |
Rivers South-East | Olaka Johnson Nwogu | PDP |
3. ’Yan takarar Majalisar Wakilai ta Tarayya
Lamba | Sunan ɗan takara | Mazaba | Jam’iyya |
1 | Bob Solomon | Abua-Odual/Ahoada East | APC |
2 | Victor C. Obuzor | Ahoada West/Ogba-Egbema-Ndoni | APC |
3 | Cyril Godwin Hart | Degema/Bonny | APC |
4 | Jack Isobo Solomon | Akuku-Toru/Asari-Toru | APC |
5 | Linda Somiari-Stewart | Okrika/Ogu-Bolo | APC |
6 | Frederick Boma Apiafi | Andoni/Opobo-Nkoro | APC |
7 | Felix Uche Nwaeke | Eleme/Tai/Oyigbo | APC |
8 | Dumnamene R. Dekor | Khana/Gokana | APC |
9 | Martin C. Amaewhule | Obio/Akpor | APC |
10 | Blessing C. Amadi | Port Harcourt II | APC |
11 | Kelechi G. Nwogu | Etche/Omuma | PDP |
12 | Arthur O. Uchendu | Ikwerre/Emohua | PDP |
13 | Achinike Okogbule-Wonodi | Port Harcourt I | PDP |
4. ’Yan takarar Majalisar Dokokin Jihar Rivers
Lamba | Sunan ɗan takara | Mazaba | Jam’iyya |
1 | Dominic I. John | Abua/Odual | PDP |
2 | Napoleon N. Ukalikpe | Ahoada East II | APC |
3 | Queen U. Tony-Williams | Ahoada East I | PDP |
4 | Reuben Izu | Ahoada West | PDP |
5 | Victor Dagogo-Jack | Akuku-Toru I | APC |
6 | Lolo I. Opuende | Akuku-Toru II | APC |
7 | Christopher K. Ofiks | Andoni | APC |
8 | Tekenari W. Granville | Asari-Toru I | APC |
9 | Enemi Alabo George | Asari-Toru II | APC |
10 | Soparagha S. Jumbo | Bonny | APC |
11 | Peters E. Abbey | Degema | APC |
12 | Aforji Igwe-Obey | Eleme | APC |
13 | Ignatius O. Onwuka | Etche I | PDP |
14 | Chimezie C. Nwankwo | Etche II | APC |
15 | Justina Emeji | Emohua | PDP |
16 | Dumle Maol | Gokana | APC |
17 | Prince Lemchi Nyeche | Ikwerre | PDP |
18 | Barile Nwakoh | Khana I | PDP |
19 | Bulabari H. Loolo | Khana II | APC |
20 | Ezebunwo L. Ejekwu | Obio/Akpor I | APC |
21 | Emilia L. Amadi | Obio/Akpor II | PDP |
22 | Okobiriari A. Davids | Ogu/Bolo | APC |
23 | Opuene T. Atekebo | Okrika | APC |
24 | Nwabochi F. Uchenna | Ogba/Egbema/Ndoni I | APC |
25 | Ijeoma Ezekwe | Ogba/Egbema/Ndoni II | PDP |
26 | Enyinna S. Nwankwo | Omuma | PDP |
27 | Kenneth G. Minimah | Opobo/Nkoro | APC |
28 | Gerald C. Oforji | Oyigbo | APC |
29 | Solomon Wami | Port Harcourt I | APC |
30 | Tonye Smart Adoki | Port Harcourt II | APC |
31 | Azeru Opara | Port Harcourt III | APC |
32 | Bernard B. Ngbar | Tai | PDP |
'Dan majalisar Kano ya ce a yi Tinubu
An rahoto cewa ‘dan majalisar Bichi ya roki mutanen Kano su zabi Shugaba Bola Tinubu saboda abin da ya faru a zaben 2015.
Hon. Abubakar Kabir Bichi ya ce Muhammadu Buhari ya samu mulki ne saboda goyon bayan da Tinubu ya ba shi a wancan lokaci.
Yanzu jam’iyyar APC tana sa ran kuri’u miliyan 1 su fito daga mazabun da suke a Arewacin Kano a zaben shekara mai zuwa.
Asali: Legit.ng


