Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa Ta Duniya FIFA Ya Dura a Najeriya

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa Ta Duniya FIFA Ya Dura a Najeriya

  • Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya isa birnin Warri da ke Jihar Delta a safiyar Juma’a domin ziyarar aiki
  • Gwamna Sheriff Oborevwori ne ya tarbe shi a filin jirgin saman Osubi da ke Warri a safiyar yau Juma'a
  • Ana sa ran Infantino zai ƙaddamar da filin wasa na Warri City Stadium da kuma filin kwalejin Hussey

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Warri, Delta - Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya isa birnin Warri da ke Jihar Delta a safiyar ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamban 2026.

Infantino ya sauka ne a filin jirgin saman Osubi da ke Warri, inda gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya tarbe shi.

Shugaban FIFA ya iso Najeriya
Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta FIFA, Gianni Infantino. Hoto: FIFA.
Source: Getty Images

Abin da ya kai shugaban FIFA Warri

Ana sa ran ziyarar Infantino za ta haɗa da ƙaddamar da sabon filin wasa na Warri City Stadium da kuma filin ƙwallon ƙafa na Hussey, cewar Daily Trust..

Kara karanta wannan

Shinkafa da wake: An kafa kwamitin kamfen Tinubu da APC cike da yan adawa

Mataimakiyar shugabar kwamitin gasar ƙungiyoyin ƙasashe na maza na FIFA, Amaju Pinnick, ta bayyana cewa ziyarar ta nuna irin ƙudurin shugaban FIFA na bunƙasa ƙwallon ƙafa daga tushe.

Da yake magana a gidan talabijin na Arise TV, Pinnick ya ce mutane da dama ba za su yi tsammanin shugaban FIFA zai kai ziyara Warri ba, amma Infantino yana matuƙar son bunƙasa ƙwallon ƙafa a matakin ƙananan hukumomi da al'ummomi.

Ya bayyana cewa lokacin da ya fara karɓar Infantino daga filin jirgin sama, shugaban na FIFA ya riƙa ƙidayar mutanen da yake gani suna buga ƙwallo a kan hanya.

Pinnick ya ce daga nan ne ya ba shi labarin Hussey College, inda aka ƙara ƙarfafa ra'ayin ziyartar makarantar.

Kwalejin Hussey ta samar da 'yan Super Eagles 17

Pinnick ya bayyana cewa Hussey College ta samar da tsofaffin 'yan wasan Super Eagles guda 17, lamarin da ya nuna muhimmancin makarantar wajen bunƙasa ƙwallon ƙafa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Abin da ya fi burge Atiku idan aka taɓa Tinubu yayin amfen

Ya ce Infantino yana girmama tsofaffin gwarazan ƙwallon ƙafa, kuma yana farin cikin ganin shugaban FIFA zai ziyarci filin wasa na Warri City Stadium.

Ƙarin bayani na tafe.....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.