APC na tsaka Mai Wuya, Ana Neman Cire Sunan Dan Takararta na Gwamna a Zaben 2027
- Jam’iyyar PRP ta shigar da ƙara tana neman kotu ta ayyana cewa APC ba ta cancanci tsayar da ɗan takara a zaɓen gwamnan Rivers na 2027 ba
- Ta roƙi kotu ta umarci INEC ta cire APC da ɗan takararta daga jerin waɗanda za su fafata a zaɓen gwamnan jihar Rivers mai zuwa
- Har yanzu ba a sanya ranar sauraron ƙarar da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Fatakwal ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Jam’iyyar PRP ta roƙi Babbar Kotun Tarayya da ke Fatakwal, jihar Rivers, ta haramta wa APC shiga zaɓen gwamnan jihar na ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
Ƙarar mai lamba FHC/PH/CS/193/2026 ta kuma nemi kotun ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta cire APC da ɗan takararta daga jerin jam’iyyun siyasa da suka cancanci tsayar da ’yan takara a Rivers.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar NDC ta yi barazana ga INEC kan cire sunan Aminu Gwarzo daga takara a Kano

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa PRP ce ta shigar da ƙarar tare da ɗan takararta na gwamna, Hon. Kieghe Nature Dumale.
Sun shigar da INEC a matsayin wanda ake ƙara na farko, yayin da APC take a matsayin wadda ake ƙara ta biyu.
Dalilin shigar da ƙara gaban kotu
A cikin takardar kara da ta ƙunshi sakin layi 18, Dumale, wanda shi ne mai ƙara na farko, ya bayyana cewa Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a ranar 24 ga Satumba a wata ƙara da ta shafi INEC da ZLP.
Ya ce hukuncin da aka yanke a ƙarar ya shafi halascin sashe na 77(5) zuwa na 77(7) na Dokar Zaɓe ta 2026.
A cewarsa, hukuncin ya tabbatar da ikon INEC na tabbatar da bin waɗannan tanade-tanade ko kuma ɗaukar mataki kan jam’iyyun siyasa da suka saɓa musu.
Sun kuma bayyana cewa a ranar 13 ga Oktoba, INEC ta fitar da sanarwa inda ta ce ta yi amfani da hukuncin Kotun Ƙoli wajen haɗa jerin sunayen ’yan takarar gwamnan Rivers.
Dumale ya kuma yi zargin cewa Chinda Kingsley Ogundu ya yi rajistar zama mamba a APC a ranar 27 ga Afrilu, 2026, duk da cewa sunansa bai cikin jerin da jam’iyyar ta miƙa wa INEC.
A cewarsa, an miƙa wa INEC takardar shaidar zama mamba ta wucin gadi ta Chinda tare da fom ɗin INEC EC9. An gabatar da takardar a matsayin shaida mai alamar ‘F’.
Masu ƙarar sun kuma ce, bisa rajistar mambobin PDP a ƙaramar hukumar Obio/Akpor ta jihar Rivers, Chinda mamba ne a PDP.
Sun ce sunansa yana lamba ta 74917 a cikin rajistar da aka gabatar wa INEC bisa sabon jadawalin ayyukan babban zaɓen 2027.

Source: Getty Images
Abin da PRP ke nema a kotu
Masu ƙarar, ta hannun tawagar lauyoyinsu ƙarƙashin jagorancin Dr. Doueyi Fiderikumo, suna neman kotun ta ba su manyan buƙatu biyu.
Na farko, suna neman kotun ta ayyana cewa APC ba ta cancanci tsayar da ɗan takarar gwamnan jihar Rivers a zaɓen da za a gudanar ranar 6 ga Fabrairu, 2027 ba.
Na biyu, suna neman kotun ta umarci INEC da ta cire APC da ɗan takararta daga jerin jam’iyyun siyasa da suka cancanci tsayar da ’yan takara a zaɓen. Har zuwa yanzu, ba a sanya ranar sauraron ƙarar ba.
Fubara ya ce Wike ne jagora
Kun ji cewa gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya buƙaci magoya bayan Rainbow Coalition su daina kiransa shugabansu ko jagora.
Fubara ya bayyana cewa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja shi ne jagoran ƙungiyar Rainbow Coalition kuma jagora a Rivers.
Asali: Legit.ng

