Gwamna Ya Mayar da Kansa Baya, Ya Fadi Mai Gidansa da Yan Jihar Ya Kamata Su Bi
- Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya buƙaci magoya bayan Rainbow Coalition su daina kiransa shugabansu ko jagora
- Fubara ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da ’yan takarar ƙungiyar a Rivers, inda Wike, ministan Abuja, ya halarta
- Gwamnan ya ce dukkan ɓangarorin siyasar da suka haɗu ƙarƙashin ƙungiyar ya kamata su amince da shugabanci guda, su guji rarrabuwar kawuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya fadi muhimmancin da Nyesom Wike ke da shi.
Fubara ya bayyana cewa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja shi ne jagoran ƙungiyar Rainbow Coalition.

Source: Facebook
Fubara ya shawarci masoyansa a Rivers
Fubara ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayan ƙungiyar a wajen ƙaddamar da ’yan takararta a Port Harcourt, babban birnin Rivers, inda Wike yake halarta, cewar TheCable.
Gwamnan ya buƙaci mambobin Rainbow Coalition su daina kiran wasu ’yan siyasa daban-daban shugabanninsu, yana mai bayyana Wike a matsayin “jagoran Rainbow Coalition” kuma mai gidansa.
Fubara ya ce wasu mambobin da suka goyi bayansa lokacin rikicin siyasar Rivers har yanzu suna ɗaukar kansu a matsayin mabiya ɓangarori masu shugabanci daban-daban, duk da sabon tsarin siyasar da aka cimma.

Source: Instagram
Fubara ya nemi hadin kai don cimma nasara
Ya ce dukkan ƙungiyoyin sun haɗu a ƙarƙashin inuwa guda, don haka bai kamata su ci gaba da ɗaukar kansu a matsayin sansanonin siyasa daban-daban ba.
“Ina sane da cewa akwai wasu matsaloli, domin wasu mutanen da suka biyo ni lokacin da muka yi rikici, idan suna taro, za ka ji suna cewa, ‘shugabana, shugabana.
“Yanzu muna gida guda. Kuma da yake muna gida guda, babu batun wanda ne shugaba.”
- Cewr Fubara
Gwamnan ya bayyana cewa duk da wasu mambobi na iya ci gaba da kallonsa a matsayin shugabansu, ya kamata su amince da matsayin Wike a cikin ƙungiyar, cewar Punch.
Ya buƙaci mambobin su warware matsalar tare da ci gaba a matsayin iyali guda na siyasa, yana mai gargaɗin kada su yi kalaman da za su nuna cewa akwai shugabanci fiye da ɗaya a ƙungiyar.
“Wataƙila ni ne Oga ɗinku, amma yanzu muna da shugaba guda, don haka, ina roƙonku daga yanzu a warware wannan matsalar ta ‘shugabana, shugabana, shugabana’ a nan."
- In ji Fubara.
Wannan na zuwa ne bayan rikicin siyasa da ya barke a jihar tsakanin Wike da Fubara kafin daga bisani a samu maslaha.
Wike ya ce Amaechi bai cancanta ba
Mun ba ku labarin cewa Nyesom Wike ya bukaci ’yan Najeriya da kada su zaɓi tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, a kowane muƙami bisa zargin almundahanar kuɗaɗe.
Wike ya yi zargin cewa ba a san inda Dala miliyan 308 da aka samu daga sayar da tashar wutar lantarki ta Afam a shekarar 2014 suka shiga ba.
Ministan ya kuma tambayi inda aka kai Dala miliyan 49 na asibitin Justice Karibi-Whyte da kuma Naira biliyan 68 na aikin jirgin ƙasa na cikin gari.
Asali: Legit.ng

