Alamu Sun Bayyana a Kano, Tinubu Zai Sha Mamakin Kuri'un da zai Samu a Arewa a Zaben 2027

Alamu Sun Bayyana a Kano, Tinubu Zai Sha Mamakin Kuri'un da zai Samu a Arewa a Zaben 2027

  • Darakta Janar na kungiyar Arewa for Asiwaju, Muhammadu Badaru Abubakar, ya ƙaddamar da jakadun matasan Kano 528
  • Tsohon ministan tsaron ya yi hasashen cewa duba da abin da ya gani a Kano, Arewa za ta ba Shugaba Bola Tinubu ƙuri’u masu yawa a zaɓen 2027
  • An ɗora wa matasan alhakin yaɗa ayyukan Tinubu a faɗin ƙananan hukumomi 44 da mazaɓu 484 na jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Darakta Janar na ƙungiyar Arewa for Asiwaju, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar, ya ƙaddamar da jakadun matasa 528 a a jihar Kano ranar Laraba.

Badaru, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya yi hasashen cewa Arewa za ta ba Shugaba Bola Tinubu ƙuri’u masu tarin yawa a zaɓen 2027.

Gwarzo.
Shugaban A4A na jihar Kano, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo a wurin kaddamar da jakadun matasa Hoto: Arewaforasiwaju
Source: Facebook

Ya bayyana wannan hasashe ne yayin da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar na kaddamar da jakadun matasa a Kano, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

‘Dan majalisar Kano ya tuno alherin da Tinubu ya yi wa Buhari a kokarin tallar APC

Yan Arewa su sake zaben Tinubu

Badaru Abubakar, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro, ya ce ana sa ran matasan za su zagaya lunguna da saƙo na ƙananan hukumomi 44 na jihar domin yaɗa ayyukan alheri da gwamnatin Tinubu ta gudanar gabanin babban zaɓen 2027.

Ya ce aikin jakadun shi ne ziyartar mazaɓu 484 da ke cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano domin wayar da kan jama’a game da ayyukan shugaban ƙasar, waɗanda ya ce ba farfaganda ba ne.

Badaru ya bayyana cewa matasa su ne ginshiƙin samun nasara a zaɓe, yana mai cewa yadda matasa da dama suka fito tare da nuna goyon bayansu a taron ya ƙara tabbatar masa da cewa nasarar Tinubu a 2027 ta tabbata.

“Yawan matasan da suka fito cikin farin ciki domin halartar wannan shiri ya ƙara mana kwarin gwiwa sosai. Ban da haka, mun daɗe da sanin cewa Arewa na tare da shugaban ƙasa," in ji shi.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Bukatar da Shettima ya nema wajen 'yan Arewa kan tazarcen Tinubu

Yadda A4A za ta tallata Tinubu

Tsohon ministan tsaron ya ƙara da cewa ƙungiyar ba za ta buƙaci farfaganda wajen yaƙin neman zaɓenta ba, domin za ta nuna wa jama’a ayyukan da aka gudanar a Arewa da kuma shirye-shiryen tallafa wa jama’a domin samun ƙarin ƙuri’u ga Tinubu.

Ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a ƙaddamar da reshen ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A) na Abuja da sauran ofisoshin hulɗa a sassan ƙasar.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana magana da wasu baki da suka kai masa ziyara a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

An zaɓi matasa masu nagarta

Da yake nasa jawabin, shugaban A4A reshen Kani kuma tsohon ƙaramin ministan gidaje, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, ya ce an zakuli matasan cikin tsanaki domin tabbatar da cewa an haɗa waɗanda ke da nagarta da mutunci.

Gwarzo ya ce za su fito da muhimman ayyukan da aka gudanar a faɗin Arewa, domin nuna wa jama’a cewa shugaban ƙasar ya cancanci samun ƙuri’u masu yawa daga yankin.

Abubuwan da za su taimaki APC a Kano

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ce Kano da jihohin Arewa 6 za su sake zaɓen Tinubu a 2027, ya faɗi dalili

Kun ji cewa Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada ta tarayya, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana abubuwan da za su taimaki APC a jihar Kano.

Doguwa ya ce sabon sauyin siyasa da kuma karuwar hadin kai a cikin APC za su sanya jam’iyyar cikin kyakkyawan matsayi na samun nasara a Jihar Kano a babban zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262