Jigo a APC Ya Hango Mamakin da Za a Sha a Arewa Saboda Tinubu a Zaben 2027
- Ali Bukar Dalori ya ce Shugaba Bola Tinubu zai samu ƙuri'u masu tarin yawa a jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja a zaɓen 2027
- Ya kare matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa gwamnatin Tinubu ta gaji matsalolin tattalin arziki da bashin ƙasashen waje daga gwamnatin baya
- Dalori ya lissafa ayyukan tituna, gadoji da asibitoci da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a Arewa maso Gabas da sauran sassan Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa mai kula da Arewa, Dakta Ali Bukar Dalori, ya yi watsi da shakku kan yiwuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu samun ƙuri'u masu yawa a yankin Arewa a zaɓen 2027.
Dalori ya yi hasashen cewa Tinubu zai samu gagarumar nasara a dukkan jihohin Arewa 19 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri, gabanin ziyarar shugaban ƙasar domin ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan raya yankin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Dalilin da ya sa ake ganin Tinubu zai yi nasara
Dalori ya ce matsalolin tattalin arziki da suka haɗa da tsadar rayuwa ba za su hana al'ummar Arewa sake zaɓar Tinubu ba.
Ya kare matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta ɗauka, yana mai cewa hakan ya zama dole saboda halin da tattalin arzikin ƙasar yake ciki lokacin da gwamnatin ta karɓi mulki.
A cewarsa, annobar COVID-19 ta yi wa tattalin arzikin Najeriya mummunan illa, har ta kai ga gwamnatin baya ta sayar da ɗanyen man fetur tun kafin lokacin da za a haƙo shi.
Ya kuma yi zargin cewa gwamnatin baya ta tara dimbin basussukan ƙasashen waje domin gudanar da ayyukanta.
Dalori ya ce gwamnatin Tinubu, wadda ta ɗauki kanta a matsayin mai ci gaba da wasu manufofin gwamnati, ba ta da wani zaɓi face cire tallafin domin fara aiwatar da shirinta.
Ya ƙara da cewa, da yardar Allah, ƙuri'un da al'ummar Arewa za su bai wa Tinubu a 2027 za su ba masu sukar sa mamaki.
Ayyukan raya ƙasa da gwamnatin APC ke yi
Domin ƙarfafa hujjojinsa, mataimakin shugaban APC ɗin ya lissafa wasu manyan ayyukan gine-gine da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a Arewa maso Gabas da sauran yankunan Arewa.
Ya ambaci aikin faɗaɗa hanyar Gombe zuwa Biu da Maiduguri zuwa tagwayen hanya, da kuma hanyar Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja.
Sauran ayyukan sun haɗa da hanyoyin Maiduguri zuwa Dikwa zuwa Gamboru Ngala, da Maiduguri zuwa Monguno.
Ya kuma ambaci aikin sake gina hanyoyin Gombe zuwa Dukku, Gombe zuwa Bajoga zuwa Potiskum, da Gombe zuwa Yola.
Ya yi magana kan tarukan kamfen ɗin APC
Dalori ya kuma yi nuni da yawan mutanen da suka fito wajen tarukan fara kamfen ɗin shugaban ƙasa na APC a wasu jihohin Arewa.
Ya ambaci jihohin Kaduna, Jigawa, Kebbi, Sokoto da Plateau, tare da wasu jihohin yankin, a matsayin wuraren da ya ce an samu fitowar jama'a sosai.

Kara karanta wannan
APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu
A cewarsa, wannan fitowar jama'a na nuna cewa nasarar Tinubu da APC a zaɓen 2027 abu ne tabbatacce.

Source: Facebook
An janye goyon baya ga Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiyar siyasa mai suna APC Northern Youths Forum ta bayyana cewa za ta janye goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmad Tinubu a ƙoƙarinsa na neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen 2027.
Kungiyar ta jaddada cewa mambobinta ba za su fice daga jam’iyyar APC mai mulki ba, amma za su yi aiki wajen ganin Tinubu bai sake komawa kan karagar mulki ba a Kano da sauran jihohin Arewa.
Asali: Legit.ng

