Tinubu Ya Yi Alkawarin Gyare-gyare da Inganta Jin Daɗin Aikin ’Yan Sanda

Tinubu Ya Yi Alkawarin Gyare-gyare da Inganta Jin Daɗin Aikin ’Yan Sanda

  • Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi alkawarin inganta jin daɗin jami’an ’yan sanda da ƙarfafa rundunar ta fannoni da yawa
  • Ya ce dukkan majalisun dokokin jihohi 36 sun amince da kudirin kafa rundunar ’yan sandan jihohi nan ba da jimawa ba
  • Jami’an ’yan sanda 845 sun kammala horo a makarantar horas da ’yan sanda ta Wudil da ke jihar Kano a Arewa maso Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wudil, Jihar Kano - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin ci gaba da gyare-gyare a rundunar ’yan sandan ƙasar domin ƙarfafa aikinta da inganta jin daɗin jami’anta.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 22 ga Nuwamban 2026, yayin bikin yaye ɗaliban rukunin horo na takwas a Makarantar Horas da ’Yan Sanda ta Najeriya da ke Wudil, jihar Kano.

Shugaban ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da samar da tallafin da ya dace domin ƙarfafa rundunar da kuma inganta yanayin aikin jami’anta.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake dawo da alkawarin da ya dauka a baya, ya roki yan Najeriya

Ya jaddada cewa nasarar gyare-gyaren za ta kuma dogara ne da ƙwazon da sabbin jami’an za su nuna wajen gudanar da aikinsu.

Shugaba Tinubu kan aikin 'yan sanda
Tinubu kan batun gyara harkokin jin dadin 'yan sanda | Hoto: @OfficialABAT
Source: Getty Images

Jihohi 36 sun amince da ’yan sandan jihohi

A cikin jawabinsa, Tinubu ya yi tsokaci kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya da zai share fagen kafa rundunar ’yan sandan jihohi.

Ya ce majalisun dokokin jihohi 36 sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin da ya tanadi kafa wannan runduna.

A cewar bayanin da aka gabatar, amincewar ta zarce mafi ƙarancin kaso biyu bisa uku da sashe na 9(2) na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya tabbatar da cewa Tinubu zai rattaba hannu kan kudirin a wani biki na musamman. Wannan ne matakin ƙarshe da aka bayyana na kammala tsarin kafa rundunar ’yan sandan jihohi.

Jami’ai 845 sun kammala horo

Jami’an ’yan sanda masu muƙamin ASP guda 845 ne aka ba muƙamansu a yayin bikin, kamar yadda rahoto ya bayyana ranar Asabar.

Wasu daga cikinsu sun kuma samu lambobin yabo saboda bajintar da suka nuna a lokacin karatu da horo.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Kwamandan makarantar, AIG Auwal Muhammad, ya bayyana bikin a matsayin wani lokaci na nuna ladabi da shirin sadaukar da kai ga ƙasa. Ya kuma gode wa gwamnatin tarayya bisa tallafin da take bai wa shirye-shiryen karatu na makarantar.

Tinubu ya gargaɗi sabbin jami’ai

Tinubu ya buƙaci sabbin jami’an da su riƙa bin kundin tsarin mulki, mutunta haƙƙoƙin ƴan ƙasa da kuma guje wa amfani da muƙamansu domin amfanin kansu.

Ya tunatar da su cewa sanya kayan aikin ɗan sanda na nufin ɗaukar amanar jama'a.

Shugaban ya ce abin da zai nuna nasarar aikinsu ba matsayin da suka kai ba ne, sai dai rayukan da suka kare, al'ummomin da suka samar wa da tsaro da kuma amincewar da jama'a suka yi da su.

Ku yi aikinku da tawali'u

Ya kuma buƙaci jami'an su gudanar da ayyukansu cikin tawali'u, gaskiya da kishin ƙasa.

Tinubu ya ƙarfafa su da su rungumi amfani da fasaha, tattara bayanan sirri da haɗin gwiwa da al'umma domin tunkarar sauye-sauyen ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta.

Bikin kammala karatun ya kawo ƙarshen shekaru biyar na horo mai zurfi a fannin ilimi, ƙwarewar aikin ɗan sanda da kuma motsa jiki.

Shugaban ya gode wa iyalan ɗaliban da suka kammala horon da kuma shugabannin makarantar, malamai da sauran ma'aikata bisa gudummawar da suka bayar wajen horar da sabbin jami'an rundunar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng