Akpabio Ya Tona Asirin Masu Sukar Tinubu a Kafafen Sada Zumunta

Akpabio Ya Tona Asirin Masu Sukar Tinubu a Kafafen Sada Zumunta

  • Godswill Akpabio ya yi zargin cewa ana biyan wasu mutane kuɗi domin su riƙa sukar Shugaba Bola Tinubu da magoya bayansa
  • Shugaban Majalisar Dattawan ya buƙaci matasan Arewa su ƙara wayar da kan jama’a domin neman goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027
  • Akpabio ya kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, ciki har da sauye-sauyen haraji da ƙoƙarin rage dogaro da man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi zargin cewa ana biyan wasu mutane kuɗi domin su riƙa sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da magoya bayansa a kafafen sada zumunta.

Akpabio ya kuma buƙaci matasan Arewa su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da neman goyon baya ga Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Akpabio ya kare Shugaba Tinubu
Godswill Akpabio tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Godswill Obot Akpabio, Bayo Onanuga
Source: Twitter

Vanguard ta ce ya yi wannan kira ne a ranar Laraba, 28 ga watan Oktoban 2026 lokacin da wata ƙungiyar matasa ta Arewa mai suna Arewa Revival Project, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Mustafa Ibrahim, ta kai masa ziyarar girmamawa a ofishinsa.

Kara karanta wannan

Ana batun shirin dage zaben 2027, majalisa ta gayyaci shugaban INEC

Ƙungiyar matasan Arewa ta karrama Akpabio

Ƙungiyar, wadda mambobinta suka fito daga jihohin Arewa 19, ta bai wa Akpabio lambar yabo domin karrama shi bisa gudummawar da yake bayarwa wajen gina ƙasa.

Da yake godiya kan wannan karramawa, shugaban Majalisar Dattawan ya buƙaci mambobin ƙungiyar su koma matakin tushe domin wayar da kan jama’a game da buƙatar ci gaba da mulkin jam’iyyar APC.

Ya ce yana da muhimmanci ’yan Najeriya su fahimci amfanin ci gaba da manufofin gwamnati maimakon sauya alkibla.

“Duk abin da muke yi a yau, muna yin sa ne domin tabbatar da kwanciyar hankalin makomarku da kuma dorewar Najeriya. Saboda haka, yana da kyau ku fahimci hakan.” In ji shi.

Zargin Akpabio kan masu sukar Tinubu?

Tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom ya yi gargaɗin cewa matasan da ke goyon bayan gwamnati na iya fuskantar ƙalubale wajen fafatawa da masu sukar ta a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

To fa: ADC ta fallasa makarkashiyar da ake shiryawa kan zaben 2027, ta ja kunnen Tinubu

"Ba zai kasance da sauƙi a gare ku ba, domin yawancin waɗanda ke kai wa shugaban ƙasa da waɗannan matasa hari a kafafen sada zumunta ana biyansu kuɗi. Amma ku ba a biyan ku.” In ji shi.

Akpabio ya ƙara da cewa yana iya yi wa matasan wuya su samu irin ƙarfin hali da lokacin da masu sukar gwamnati ke amfani da shi a kafafen sada zumunta.

Sai dai ya shawarce su da su riƙa haɗuwa lokaci zuwa lokaci domin tattauna al’amura da wayar da kan sauran matasa kan abin da ya kira gaskiya game da ayyukan gwamnati.

Ya ce bai dace mutane su riƙa kai wa gwamnatin da yake ganin tana aiki domin amfanin jama’a hari ta hanyar haifar da rashin tabbas ba.

Ya kare manufofin tattalin arzikin Tinubu

Akpabio ya kuma kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, ciki har da sauye-sauyen dokokin haraji da ake aiwatarwa.

A cewarsa, gwamnatin na ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da bunƙasa wasu sassan tattalin arziki domin rage dogaro da man fetur.

Akpabio ya yi maganar Tinubu
Sanata Godswill Akpabio a zauren majalisar dattawa Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Atiku ya mika bukata ga Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya rika fitar da hotuna da bidiyoyi a kullum domin tabbatar da cewa yana Makkah yana gudanar da ibadar Umrah.

Tsohon mataimakin shugaban kasar kuma babban mai adawa da Tinubu ya bayyana shakku kan ainihin inda shugaban ƙasar zai je.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng