Kofa Ya Ce APC za Ta Lashe Kano Baki Daya, Kwankwaso zai Rasa Kujeru a 2027
- Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce APC ba za ta bar wa jam’iyyun adawa kujera ko daya a Kano a 2027 ba
- Jibrin Kofa ya ce APC za ta lashe zaben shugaban kasa da sauran zabukan mukamai daban-daban saboda karfin shugabanninta da tsarinta
- Hakan na zuwa ne yayin da hukumar INEC ke shirin wallafa bayanan ‘yan takarar gwamna da na majalisun dokokin jihohi gabanin zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba za ta bar wa jam’iyyun adawa kujera ko daya a jihar Kano ba a babban zaben shekarar 2027.
Jibrin Kofa, wanda aka fi sani da Jarman Bebeji, ya bayyana haka ne yayin wani taro na musamman da ya hada shugabannin APC da wakilan rumfunan zabe daga kananan hukumomin Kiru da Bebeji.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa ya ce jam’iyyar APC na da yakinin cewa za ta rike kujerar shugaban kasa tare da lashe sauran mukaman zabe da za a fafata a kansu a jihar Kano.
Batun nasarar APC a Kano
Dan majalisar ya ce karfin tsarin siyasar APC da yawan manyan shugabanninta a Kano za su taimaka wa jam’iyyar wajen samun nasara a babban zaben 2027.
Jibrin Kofa ya ce:
"Na rantse da Allah, a Kano, idan babban zaben 2027 ya zo, ba za mu bar musu kujera ko daya ba. Na sake cewa, APC ba za ta bar wa jam’iyyun adawa kujera ko daya ba."
Ya ce APC za ta lashe zaben shugaban kasa a jihar Kano, yana mai cewa shugabannin jam’iyyar sun fara aiki domin kara tabbatar da goyon bayan jama’a gabanin zaben.
Ya amince cewa rikicin cikin gida ya taba zama babban kalubale ga APC, amma ya ce ana kokarin shawo kan matsalar tare da kara hada kan mambobin jam’iyyar.

Kara karanta wannan
"Ka shirya barin Aso Villa"; Melaye ya fadi dabarar ADC ta kifar da Tinubu a 2027
Manyan 'yan APC a Kano
Jibrin Kofa ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, suna daga cikin manyan mutanen da za su taimaka wajen karfafa tsarin APC a jihar.
Ya kuma ambaci mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin da tsohon gwamna Ibrahim Shekarau.

Source: Facebook
Sauran wadanda ya ambata sun hada da Sanata Kawu Sumaila da Sanata Rufai Hanga, tare da sauran ‘yan takarar majalisun dokoki na kasa da na jiha.
Za a fadi bayanan ‘yan takara
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, za ta wallafa bayanan ‘yan takarar gwamna da na majalisun dokokin jihohi gabanin babban zaben 2027.
Mataimakin daraktan yada labarai na INEC, Wilfred Osilama Ifogah, ya ce ranar da hukumar ta tsara domin wallafa bayanan ‘yan takarar ba za a sauya ta ba.
Ya ce an tsara hakan ne bisa tanadin sashe na 29(3) na dokar zabe, yayin da jam’iyyun siyasa ke shirin fara yakin neman zabe domin ‘yan takarar gwamna da na majalisun dokokin jihohi daga ranar 9 ga watan Satumbar 2026.
Asali: Legit.ng
