Wike Ya Faɗi Abin da Zai ana Obi Zama Shugaban Kasa, Ya Tuna Mummunan Halinsa 1
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana Peter Obi a matsayin mutum mai rowa, yana mai cewa bai cancanci shugabancin Najeriya ba
- Wike ya soki Obi kan ɗaukar jakarsa da kansa, yana mai cewa shahararsa a kafafen sada zumunta ba ta tabbatar da ƙwarewar shugabanci ba
- Ministan ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu da APC a zaɓen 2027, tare da zargin almundahanar kuɗi a wasu ayyukan gwamnatin Rivers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya caccaki dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi.
Wike ya bayyana ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC Peter Obi, a matsayin mutum mai rowa wanda bai cancanci jagorantar Najeriya ba.

Source: UGC
Wike ya yi wa Peter Obi ba'a
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar Bonny da ke Jihar Rivers, inda ya yi wa tsohon gwamnan Anambra ba’a kan ɗaukar jakarsa da kansa, cewar Punch.
Ya bayyana Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na kafafen sada zumunta, yana mai cewa shahara a intanet ba ta maye gurbin ƙwarewa da ƙarfin ikon gudanar da mulkin ƙasa.
Ya ce:
“Idan ka taɓa zama gwamna, bai kamata ka zama mai rowa har ka kasa ɗaukar mataimaki na musamman da zai riƙa ɗaukar maka jaka ba. Kana son nuna cewa kai da kanka kake ɗaukar jakarka. Ba ma son irin wannan mai rowa ya zama shugaban ƙasa.
“Gaskiya ne, na ba shi matsayin shugaban ƙasar kafafen sada zumunta. Idan za a zaɓi wanda zai zama shugaban ƙasar kafafen sada zumunta, zan zaɓe shi. Amma idan batun mulkin Najeriya ne, sam ba zai yiwu ba."

Source: Facebook
Wike ya kalubalanci mulkin Obi
Ministan ya kuma yi tambayoyi kan tarihin mulkin Obi a matsayin gwamnan Anambra, yana mai cewa ya kamata a yi amfani da ayyukan gwamna mai ci, Chukwuma Soludo, wajen tantance irin nasarorin da gwamnatin tsohon gwamnan ta samu.
Haka kuma, ya soki ’yan siyasar da ke sauya jam’iyya saboda rikice-rikicen cikin gida, yana mai cewa shugabanci na buƙatar iya fuskantar ƙalubale maimakon guduwa daga gare su.
“Ta yaya za ka magance matsalolin ƙasar nan? Shin kun ga lokacin da aka samu matsala a PDP? Na gudu ne? Na kayar da su."
in ji shi.
Wike ya nuna shakku kan tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC da kuma amincin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya ce ya san shi tun lokacin da suke jam’iyyar PDP.
Ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC, yana mai cewa APC ce jam’iyyar da zai mara wa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, cewar Vanguard.
Wike ya magantu kan takarar Pantami
An ji cewa Nyesom Wike ya yi ikirarin cewa bai taba haduwa da tsohon ministan sadarwa kuma dan takarar PDP a jihar Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami ba.
Ministan Abuja ya bayyana cewa gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya na zarginsa da goyon bayan takarar gwamna da Pantami ke yi a PDP.
Wannan na zuwa ne yayin da Wike ke .usayar yawu da wasu daga cikin gwamnonin APC, wadanda ba su goyon bayan gamayyar da ya kirkiro.
Asali: Legit.ng

