2027: Gwamna Ya Jawo wa Mawaki Davido Matsala da Ya Goyi Bayan Tinubu

2027: Gwamna Ya Jawo wa Mawaki Davido Matsala da Ya Goyi Bayan Tinubu

  • Wasu ’yan Najeriya sun yi barazanar kaurace wa bikin rawa na Davido da za a yi a watan Disamba a Lagos
  • Davido ya sanar da zai gudanar da kide-kide har dare uku a National Theatre da ke Lagos daga 17 zuwa 19 ga Disamba, 2026
  • Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun zargi Davido da munafunci, yayin da wasu suka kare shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wasu ’yan Najeriya sun yi barazanar kaurace wa wasan mawaki Davido na dare uku da zai gudanar a Lagos a watan Disamba.

Wannan barazana ya zo ne bayan Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

Masoya za su kaurace wa wasan Davido saboda alakarsu da Tinubu
Gwamna Ademola Adeleke da dansa, mawaki Davido. Hoto: Davido.
Source: Twitter

Martanin ya biyo bayan naɗin da aka yi wa Adeleke a matsayin mai kula da kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa na Tinubu a Osun a 2027, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

'Nadamar da APC za ta yi a ranar zabe': Kwankwaso ya jaddada kwarin guiwarsu

Adeleke ya nuna goyon baya ga Tinubu

Wannan lamari da ya ba wasu magoya baya mamaki saboda gwamnan yana jam’iyyar Accord ce da ke adawa.

A kwanakin nan, Adeleke ya bayyana goyon bayansa ga shugaban ƙasar yayin ƙaddamar da kwamitin kamfen ɗin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.

Gwamnan ya ce Tinubu na buƙatar ƙarin shekaru huɗu domin ƙarfafa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta fara.

Bikin da Davido ya shirya a Lagos

Davido ya sanar a shafinsa na X ranar Alhamis cewa zai yi kide-kide har dare uku a jere a National Theatre da ke Lagos, daga 17 zuwa 19 ga Disamba.

An sanya wa kide-kiden sunan Oriadè: The Residency', Za su nuna dawowar mawakin gida, tare da bikin cika shekaru 15 da fara harkar waƙa.

A cewar mawakin, zai rera waƙoƙi daga sabon kundinsa mai suna Oriadè, tare da wasu waƙoƙin da ya fitar a kundinansa na baya.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun maida martani da Tinubu ya ce ba zai iya zuwa kamfe wasu jihohi ba

Sai dai sanarwar ta jawo suka daga wasu masu amfani da kafafen sada zumunta waɗanda ba su amince da goyon bayan kawun mawakin ga Tinubu ba.

Wasu sun yi alƙawarin ba za su sayi tikitin shiga kide-kiden ba, yayin da wasu suka yi ba’a cewa ya dogara da ’yan uwansa da APC wajen cika wurin taron.

An sake tona tsohon saƙon Davido

Rigimar ta kuma dawo da tattaunawa kan tsofaffin kalaman Davido da ya yi kan APC a lokacin zaɓen gwamnan Osun.

Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi amfani da saƙon wajen tambayar bambancin matsayin siyasar da mawaki Davido ya nuna a baya da kuma matakin kawunsa na goyon bayan shugaban APC.

Wasu sun zargi mawakin da munafunci saboda ya yi shiru yayin da Adeleke ke fito-na-fito wajen neman goyon bayan Tinubu.

Wasu kuma sun soki iyalan Adeleke, suna cewa matakin gwamnan ya yi watsi da sadaukarwar da magoya bayansa suka yi a lokacin kamfen ɗin da ya kai shi kan mulki.

Sai dai wasu sun buƙaci jama’a su bambanta Davido da zaɓin siyasar kawunsa, suna mai cewa bai kamata a hukunta mawakin kan shawarar da bai yanke ba.

Kara karanta wannan

Jerin jihohi 12 da Shugaba Tinubu zai iya zuwa kamfe kafin babban zaben 2027

Gwamnatin Edo ta yi wa Davido tatas

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Edo ta ba Davido shawara kan yunkurinsa na kai korafi ga Shugaba Donald Trump kan zaben gwamnan Osun.

Kwamishinan yada labaran jihar Edo ya soki matakin Davido na neman Trump ya sa ido kan zaben gwamnan Osun.

Kassim Afegbua ya ce sakamakon karatun Gwamna Okpebholo da ake yadawa a intanet na bogi ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.