Yan Najeriya Sun Maida Martani da Tinubu Ya Ce ba Zai Iya zuwa Kamfe Wasu Jihohi ba

Yan Najeriya Sun Maida Martani da Tinubu Ya Ce ba Zai Iya zuwa Kamfe Wasu Jihohi ba

  • Matakin Shugaba Bola Tinubu na takaita halartar tarukan kamfen gabanin zaɓen 2027 ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya
  • Wani ɗan Najeriya, Aliu Eke Balarebe, ya danganta matakin da matsalar tsaro, fushin jama'a kan tsadar rayuwa da yanayin lafiyar shugaban ƙasar
  • Tinubu ya ce yana son mayar da hankali kan gudanar da mulki da kuma al'amuran tattalin arzikin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Matakin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na takaita halartar tarukan yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen 2027 ya jawo martani daga 'yan Najeriya.

Wasu dai na ganin ya dauki wannan mataki ne saboda gujewa matsalar tsaro, fushin jama'a kan tsadar rayuwa da kuma yanayin lafiyar mai girma shugaban kasa.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a wurin taro Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Leadership ta kawo rahoton cewa Tinubu ya shaida wa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC cewa kada su yi tsammanin zai riƙa raka su zuwa dukkan tarukan kamfen a jihohin Najeriya gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Jerin jihohi 12 da Shugaba Tinubu zai iya zuwa kamfe kafin babban zaben 2027

Tinubu ya ce kawai buƙatar mayar da hankali kan gudanar da mulki da kuma nauyin da ke kan ƙasar na tattalin arziki.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da kwamitin kamfen a Abuja, inda ya buƙaci mambobinta su kai saƙon jam'iyyar APC ga 'yan Najeriya a faɗin jihohi da ƙananan hukumomi,

Yan Najeriya sun yi martani ga Tinubu

Yan Najeriya da suka tofa albarkacin bakunansu, sun nuna cewa da alama Tinubu ya fake ne da ayyuka, amma ba su ne dalilin da ba zai je wasu jihohi kamfe ba.

Wani ɗan Najeriya mai suna Aliu Eke Balarebe ya yi iƙirarin cewa shugaban ƙasar na iya fuskantar ƙalubale wajen zirga-zirga a faɗin ƙasar domin kamfen, saboda yawaitar matsalar tsaro da kuma rashin gamsuwar jama'a da manufofin gwamnatinsa.

Balarebe ya bayyana matsalar tsaro, fushin jama'a kan tsadar rayuwa da kuma damuwa game da lafiyar shugaban ƙasar da ƙarfinsa a matsayin dalilai uku da ka iya sa Tinubu ya yanke shawarar kin zuwa kamfe.

Kara karanta wannan

Ana zargin Tinubu ba shi da lafiya da da ya yi wasu maganganu a Abuja

“Akwai dalilai da dama, amma manyan abubuwa uku ne suka bayyana dalilin da ya sa ba zai iya yin tafiye-tafiye ba. Na farko shi ne rashin tsaro. Babu yadda zai iya zuwa waɗannan jihohi saboda akwai matsalar tsaro sosai.”

Fushin jama'a kan tsadar rayuwa

Balarebe ya kuma nuna cewa rashin gamsuwar jama'a da manufofin gwamnatin na iya jefa shugaban ƙasar cikin suka idan ya halarci tarukan kamfen a faɗin Najeriya.

Ya kuma nuna shakku kan lafiyar shugaban ƙasar da kuma ƙarfinsa na jiki wajen shiga dogon jadawalin kamfen.

Bola Tinubu.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Shugaba Bola Tinubu da uwargidan shugaban kasa a taron APC Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Da yake martani yayin hira da Legit Hausa, wani matashi daga jihar Katsina, Sani Ahmad Dabai ya ce Tinubu ya yanke wannan shawarar ne saboda mutane a fusace suke da APC.

"Mai girma shugaban kasa ya san mutane a fusace suke da shi, matsalar tsaro, tsadar rayuwa yunwa, rashin cika alkawari duk sun tattara kan APC,ni ina ganin wannan ne dalilan da ba zai yi yawon kamfe ba," in ji shi.

Jihohi 12 da Tinubu zai iya zuwa

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce zai fifita gudanar da mulki maimakon kamfen, kuma ba lallai ne ya halarci dukkan tarukan yaƙin neman zaɓen APC ba.

Duk da haka, an tsara cewa shugaban ƙasar zai halarci tarukan kamfen a birane 12 da ke shiyyoyin siyasa shida na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262