Jerin Jihohi 12 da Shugaba Tinubu Zai Iya zuwa Kamfe kafin Babban Zaben 2027
- Shugaba Bola Tinubu ya ce zai fifita gudanar da mulki maimakon kamfen, kuma ba lallai ne ya halarci dukkan tarukan yaƙin neman zaɓen APC ba
- Tinubu ya buƙaci shugabannin jam'iyyar da masu tsara kamfen su jagoranci wayar da kan magoya baya a jihohi da ƙananan hukumomi
- Duk da haka, an tsara cewa shugaban ƙasar zai halarci tarukan kamfen a birane 12 da ke shiyyoyin siyasa shida na Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - A wurin kaddamar da kwamitin kamfen APC, shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bayyana cewa zai fifita gudanar da mulki fiye da harkokin yaƙin neman zabe.
Shugaban kasar ya buƙaci shugabannin jam'iyyar APC da masu tsara kamfen su ɗauki nauyin wayar da kan magoya baya a jihohi da ƙananan hukumomi.

Source: Facebook
Tinubu ba zai je kowace jiha ba

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ana shirin amfani da makami mafi haɗari bayan nukiliya a yaƙin Amurka da Iran
A cewar shugaban ƙasar, Najeriya na buƙatar kulawa fiye da kowane lokaci a yanzu kuma nauyin da ke kansa ba zai tsahirta masa ba, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Bola Tinubu ya ce:
“Aiki dole ne ya ci gaba. Duk da haka, zan ware lokaci domin yin magana kai tsaye da 'yan Najeriya, yayin da ku za ku jagoranci kamfen a jihohi da ƙananan hukumomi. Don haka, ku yi haƙuri ba zan iya zuwa ko'ina tare da ku ba.”
Jihohi 12 da aka tsara zuwa Tinubu
Duk da waɗannan alƙawura na fifita gudanar da mulki, an tsara cewa Shugaba Tinubu zai halarci tarukan yaƙin neman zaɓe a birane 12 da ke shiyyoyin siyasa shida na ƙasar, yayin da APC ke shirin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Shirin rangadin, wanda zai gudana daga watan Oktoba 2026 zuwa Janairu 2027, ya haɗa da ƙaddamar da kamfen a hukumance a Kaduna da kuma babban taron rufe kamfen a Legas.
Ga biranen da ranakun da aka tsara gudanar da tarukan da ake tsammanin Tinubu zai halarta.
- Kaduna a Arewa maso Yamma — 24 ga Oktoba, 2026 (ƙaddamar da kamfen a hukumance)
- Fatakwal, jihar Ribas a Kudu maso Kudu — 7 ga Nuwamba, 2026
- Jos, jihar Filato a Arewa ta Tsakiya — 14 ga Nuwamba, 2026
- Ibadan, jihar Oyo a Kudu maso Yamma — 21 ga Nuwamba, 2026
- Maiduguri, jihar Borno a Arewa maso Gabas — 25 ga Nuwamba, 2026
- Enugu a Kudu maso Gabas — 28 ga Nuwamba, 2026
- Bauchi a Arewa maso Gabas — 29 ga Nuwamba, 2026
- Sakkwato a Arewa maso Yamma — 5 ga Disamba, 2026
- Asaba, jihar Delta a Kudu maso Kudu — 12 ga Disamba, 2026
- Kano a Arewa maso Yamma — 17 ga Disamba, 2026
- Yola, jihar Adamawa a Arewa maso Gabas — 4 ga Janairu, 2027
- Legas, Kudu maso Yamma — 9 ga Janairu, 2027 (babban taron rufe kamfen)

Kara karanta wannan
An samu akasi harshen Tinubu ya suɓuce, ya tafka kuskure a tsakiyar jama'a a Abuja

Source: Facebook
Ana sa ran APC za ta yi amfani da tarukan wajen tattaro magoya baya, tallata 'yan takararta da kuma gabatar da ayyukan da ta gudanar a mulki gabanin babban zaɓen 2027.
Tinubu ya yi subutar baki a taron APC
Kun ji cewa Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya yi subutar baki a jawabin da ya yi a wurin taron kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa a Abuja.
Shugaba Tinubu ya kira kansa gwamna maimkon shugaban kasa, lamarin da ya dan ja hankalin mahalarta taron.
Asali: Legit.ng