Rigima Ta Shiga Gwamnatin Jihar Kano tsakanin Wasu Hadiman Abba Gida Gida
- Ana zargin Salisu Yahaya Hotoro ya fusata ‘yan kungiyar SR da SSR da ke tallata gwamnatin Kano
- Shugaban kungiyar masu daukar rahoton ayyukan ya mayar da raddi ga shugaban matasan APC na jihar
- Amir Abdullahi Kima ya tuna wa matashin cewa Abba Kabir Yusuf ya nada su kuma suna tare da shi 100%
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - An samu rashin jituwa a jihar Kano da siyasa ta ke kara daukar zafi musamman a dalilin gabatowar zaben 2027.
Wannan karo rikicin cikin gida ne yake neman barkewa a tsakanin wasu rukunin masu taimaka wa gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Facebook
Shugaban matasan APC ya soki masu dauko rahoto
A wani faifan sauti da shafin Siyasarmu ta wallafa a Facebook, an ji Salisu Yahaya Hotoro yana sukar wasu hadiman gwamna.

Kara karanta wannan
Wajen rantsar da kwamitin kamfe ya zama matattarar habaici tsakanin Akpabio, Wike da gwamnoni
Ana zargin cewa Salisu Yahaya Hotoro ya soki wadanda ke rike da mukaman masu kawo rahoto da kin kare gwamnan jihar Kano.
Shugaban matasan APC na Kano ya fito yana cewa hadiman sun saba shiga rikicin gida amma ba su iya ba Abba Kabir kariya.
Matashin ‘dan siyasar ya yi tir da yadda wasu hadiman suke fake wa da sunan tsarin aiki, suna kyale ‘yan adawa suna taba Abba.
“Idan lokacin rashin mutunci ya yi, a nan ku ke sanin kun iya bin doka, kun san ka’ida.
“Yanzu tunda mai girma gwamna ba mahaifinku ba ne, ba hakkinku ba ne ku fito ku kare masa mutuncinsa.”
- Salisu Yahaya Hotoro
Ya cigaba:
“Ku je ku zauna ku yi ta barci. Wannan tsari da ku ka dauka ya yi..”
Salisu Hotoro ya fusata 'yan SR da SSR
Abin da ya bata wa wasu daga cikinsu rai shi ne zargin yadda Hotoro ya kira su masu toshasshiyar kwakwalwa da kuma basira.
Ba a dade ba sai aka ji Amir Abdullahi Kima yana maida martani a matsayinsa na shugaban ‘yan SR da SSR a gwamnatin Kano.
Amir Abdullahi Kima ya bayyana yadda sakataren gwamnati ya ba su umarni su rike neman izinin gwamna kafin su yi wani aiki.
Shugaban kungiyar masu rike da mukaman SR da SSR ya wanke mutanensa, yake cewa suna kare gwamna daga sukar ‘yan adawa.
Amir Kima ya ce ba su tsoron kowa
Sai dai ya ce, duk da haka sai ya ji shugaban matasan APC a Kano yana sukarsu tare da zargin cewa sun san kullin da ake ta shirya masu.
Ya ce duk da yadda suke yi wa gwamna Abba aiki, amma adawa wasu a cikin gida suke yi da su kuma ba su taba kawo masu wani alheri ba.
Malam Amir Kima ya yi kaca-kaca da shi, yana cewa bai kamata ya rika yi masa maganganu irin haka tunda ba shi ya ba su mukamansu ba.
Ya bada misalin yadda suka yi shari’a da Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki da kudinsu, ya ce lokacin wasu manyan hadimai ba su tare da su.
“Ba mu so mu yi magana saboda muna son nasarar mai girma gwamna. Muna kauda kai saboda ba mu son irin wannan fitina ta bullo a junanmu..
Amma lokaci ya yi da za ku sani ba tsoronku mu ke ji ba. Kuma muna kaunar Mai girma gwamna 100%.
- Amir A. Kima
An ji ya ce babu wanda mai maganar ya fi ilmi ko tunani da zai rika taba kungiyarsu, yana mai nuna bai damu da kujerar da yake rikewa ba.
Kima da ke aiki da Ma’aikatar shari’a ya kuma kara da bayyana cewa da abin hannunsu suke taimakon jama’a saboda nasarar Abba.
Salisu Hotoro ya bada hakuri?
A shafinsa na Facebook, da alama Salisu Hotoro ya nemi afuwa tare da addu’ar Allah SWT ya ba su (jam’iyyarAPC) nasara a zabe mai zuwa.
Ya rubuta yau da safe:
"Ayi hakuri kowa ya mayar da wukar don Allah, Allah ubangiji ya tabbatar mana da nasara."
Kwankwaso ya yi zancen dawo da tallafin mai
A matakin kasa, an ji labari Rabiu Musa Kwankwaso ya tabo zancen tallafin mai a gwamnatin NDC idan an ci babban zabe.
Madugun Kwankwasiyya ya ce jagororin jam’iyyarsa sun yarda cewa farashin makamashi ya yi tsada sosai a Najeriya a yanzu.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Kwankwaso ya ce NDC na iya dawo da tallafin fetur domin rage farashin man fetur a badi.
Asali: Legit.ng


