Gwamna Abba Ya Nada Sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano

Gwamna Abba Ya Nada Sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano

  • Jihar Kano ta samu sabon sakataren gwamnatin jiha biyo bayan naɗin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar Kano (SSG)
  • Naɗin na sa wanda aka sanar a ranar Asabar, zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairun 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa sabon sakataren gwamnatin jihar Kano (SSG).

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar Kano (SSG).

Gwamna Abba ya nada sabon SSG
Gwamna Abba ya nada sabon sakataren gwamnatin jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-tofa
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 8 ga watan Fabrairun 2025.

Kara karanta wannan

Abinci ya ƙare: Gwamna ya tattara duka masu muƙaman siyasa, ya kore su daga aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya naɗa sabon SSG

Naɗin Umar Farouk Ibrahim dai zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairu, 2025.

A cewar sanarwar, an zaɓi Umar Farouk Ibrahim ne saboda ƙwarewarsa da gogewarsa mai zurfi a harkokin mulki, waɗanda ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban manufofin gwamnati da tabbatar da ci gaban Kano.

Wanene Umar Farouk Ibrahim?

Umar Farouk Ibrahim ya kwashe sama da shekaru 30 yana aikin gwamnati, inda ya riƙe manyan muƙamai da suka taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da mulki da inganta tsarin gudanar da ayyukan gwamnati a jihar Kano.

Daga watan Maris 2001 zuwa Mayu 2015, Ibrahim ya yi aiki a matsayin babban sakataren bincike, tantancewa da harkokin siyasa a ofishin sakataren gwamnatin jiha.

A wannan matsayi, ya taka muhimmiyar rawa wajen nazarin manyan manufofin gwamnati, bayar da shawarwari kan hanyoyin da suka dace a aiwatar da su a ma’aikatu, sassa, da hukumomin gwamnati daban-daban.

Kara karanta wannan

Bayan Barau ya raba tallafi, Abba Kabir ya mika miliyoyi ga matasan Kano

Har ila yau, a shekarun 2013 da 2014, ya taɓa zama sakataren gwamnatin jiha na riƙon ƙwarya yayin hutun shekara-shekara.

Baya ga wadannan muƙamai, Ibrahim ya kasance sakatare na kwamitoci da dama masu muhimmanci.

Umar Farouk Ibrahim ya kammala digirinsa na farko (B.Sc.) a fannin kimiyyar siyasa daga jami’ar Ahmadu Bello (ABU) a 1985.

Baya ga haka, ya samu takardun ƙwarewa da dama waɗanda suka ƙara masa cancanta a aikinsa.

Wane fata Gwamna Abba ke yi masa?

"A matsayinsa na gogaggen jami’in gwamnati kuma tsohon babban sakataren jiha, ana sa ran Umar Farouk Ibrahim zai kawo ƙwarewa, hangen nesa, da himma wajen gudanar da ayyukan ofishin SSG."
"Ana kallon wannan naɗi a matsayin mataki mai muhimmanci na ƙarfafa mulkin gwamnati mai ci da inganta aiwatar da manufofi da shirye-shirye."
"Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cikakken gamsuwarsa da cewa wannan naɗi zai taka muhimmiyar rawa wajen cika burin gwamnatinsa na ci gaban jihar Kano."

Kara karanta wannan

El Rufa'I ya dira a kan Uba Sani saboda tsare tsofaffin jami'an gwamnatin Kaduna

- Sunusi Bature Dawakin Tofa

Gwamna Abba ya raba tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta raba tallafin miliyoyin kuɗi ga matasa.

Gwamnatin ta ba da tallafin ne na Naira miliyan 400 ga ƙungiyoyin matasa domin su rungumi harkokin noma hannu bibbiyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng