Uba Sani Ya Fadi Abin da zai Hana Arewa Karbar Mulkin Najeriya a 2027
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya buƙaci shugabannin siyasar Arewa su daina matsa lamba kan neman shugabancin ƙasa a zaɓen 2027
- Ya ce Arewa na buƙatar ingantaccen tsarin ci gaba da zai nuna shirinta na jagorantar Najeriya, maimakon neman mulki bisa dalilin kasancewa daga yankin
- Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taro a Kaduna da aka shirya domin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da sauran 'yan takarar APC a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya buƙaci shugabannin siyasar Arewa da su dakatar da neman shugabancin ƙasa a zaɓen 2027, su mayar da hankali wajen shirya yankin domin yiwuwar komawar mulki Arewa a 2031.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a wani taro da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) da wasu ƙungiyoyin farar hula suka shirya domin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da sauran 'yan takarar APC a zaɓen 2027.

Source: Facebook
The Cable ta rahoto Uba Sani ya ce ya kamata Arewa ta yi amfani da shekaru huɗu masu zuwa wajen magance ƙalubalen ci gabanta tare da samar da cikakken tsarin manufofin da za ta aiwatar idan mulkin ƙasa ya dawo yankin.
'Arewa ba ta shirya karɓar mulki ba'
Gwamnan ya ce shugabannin Arewa na buƙatar duba kansu domin tantance ko yankin ya shirya jagorantar Najeriya, yana mai cewa har yanzu babu cikakken tsarin ci gaba da zai jagoranci yankin.
Ya ce ya kamata a fara tsara wannan manufa tun yanzu domin idan mulki ya koma Arewa a 2031, yankin ya kasance cikin shirin aiwatar da manufofinsa.
Uba Sani ya ce:
“Na sha gaya musu su nuna min tsarin da suka tanada. Ya kamata mu fara aiki kan wannan tsari tun yanzu, domin idan muka nemi mulki ya dawo Arewa a 2031, mu kasance a shirye don aiwatar da shi. Amma a yanzu ba mu shirya ba saboda babu wani cikakken tsari.”

Kara karanta wannan
Bayan kamfe ya kankama, an sake neman Atiku ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2027
Uba Sani ya soki 'yan siyasa
Gwamnan ya soki 'yan siyasar da ke neman goyon bayan jama'a bisa kasancewarsu 'yan Arewa kawai, yana mai cewa bai kamata a zaɓi mutum saboda yankin da ya fito ba.
Jaridar Punch ta rahoto ya ce kamata ya yi a riƙa tantance 'yan siyasa bisa ayyukan da suka gudanar a lokacin da suke riƙe da muƙaman gwamnati.
Uba Sani ya bayyana cewa zamanin da 'yan siyasa ke samun ƙuri'a ta hanyar yin alƙawura kawai ya wuce, musamman ga waɗanda suka taɓa riƙe muƙaman gwamnati amma ba su nuna ayyukan da suka yi ba.

Source: Original
Ya buƙaci tsofaffin gwamnoni da mataimakan shugaban ƙasa da ke neman goyon bayan jama'a su bayyana irin gudummawar da suka bayar ga jihohinsu da Najeriya baki ɗaya.
INEC za ta yi zaben gwaji
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ba za a saka sunayen jam'iyyun siyasa a takardun zaɓen gwajin da za a yi ranar Asabar ba.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa takardun za su kasance na kwaikwayo ne kawai, ba tare da sunayen jam'iyyun siyasa masu rijista ba.
Rahoto ya nuna cewa Joash Amupitan ya ce za a yi amfani da gwajin wajen tantance ingancin na'urorin BVAS, tsarin tattara bayanai da kuma aika sakamakon zaɓe.
Asali: Legit.ng

