Bayan Tinubu Must Go, ƴan APC sun bullo da Tinubu Must Go Again a Adamawa

Bayan Tinubu Must Go, ƴan APC sun bullo da Tinubu Must Go Again a Adamawa

  • Gangamin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu na 2027 ya gudanar da babban taro a Yola, jihar Adamawa, domin ƙara samun goyon baya
  • Shugaban gangamin, Farfesa Sheriff Almuhajir, ya ce gyare-gyaren tattalin arzikin Tinubu za su taimaka wajen samar da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya
  • Jam’iyyar APC a Adamawa ta tabbatar da aniyarta ta tallafa wa Tinubu a 2027, tana mai cewa ya taimaka wa jihar ta fannin more rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gangamin neman sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na 2027, mai taken Tinubu Must Go Again 2027, ya gudanar da taro a Yola, jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

2027: Dattijon Arewa da ya yi siyasa da Sardauna ya yi maganganu kan Tinubu

Masu shirya gangamin sun bayyana cewa yawan mutanen da suka halarta ya nuna irin goyon bayan da shugaban ƙasar ke da shi a yankin Arewa maso Gabas.

An yi gangamin taron Tinubu
Dandazon matasan APC karkashin Sherrif Almuhajir a jihar Adamawa. Hoto: Sherrif Almuhajir.
Source: Facebook

Jagoran kungiyar a Najeriya, Sherrif Almuhahir shi ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook a yau Alhamis 15 ga watan Oktobar 2026.

An gudanar da taron ne ranar Alhamis a Lamido Cinema, inda ya samu halartar magoya baya da wakilai daga jihohi shida na yankin Arewa maso Gabas.

Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Sheriff Almuhajir, ya ce an shirya gangamin ne bisa son rai domin nuna goyon baya ga shugaban ƙasa.

Ya ƙara da cewa gangamin na da nufin tallata manufofin gyare-gyaren da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa domin inganta tattalin arzikin Najeriya.

Almuhajir ya buƙaci ’yan Najeriya su duba ƙalubalen tattalin arzikin ƙasar ta fuskar gyare-gyaren da ake aiwatarwa, yana mai fatan manufofin za su samar da tubalin ci gaba mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

Ana shirin zaben 2027, shugaban INEC ya mika dukan lamuransa ga Ubangiji

Ya kuma bayyana abin da ya kira goyon bayan Tinubu ga bunƙasar siyasar ’yan Arewa, inda ya ce shugaban ya goyi bayan ’yan takara uku daga yankin, ciki har da biyu daga Adamawa.

Taron Tinubu Must Go Again a Adamawa
Dandazon matasan APC a taron Tinubu Must Go Again a Adamawa. Hoto: Sherrif Almuhajir.
Source: Facebook

A cewarsa, yawan matasa da sauran magoya bayan da suka halarci taron martani ne ga ikirarin cewa shugaban ƙasar ba shi da isasshen goyon baya a Arewacin Najeriya.

Shi ma da yake magana, sakataren APC na jihar Adamawa, Mustapha Atiku Ribadu, ya bayyana aniyar jam’iyyar na tattara masu zaɓe domin tallafa wa ƙoƙarin Tinubu na samun wa’adi na biyu.

Ya danganta hakan da alaƙar siyasar shugaban ƙasar da Adamawa, da kuma ayyukan more rayuwa da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a jihar.

Mataimakin shugaban APC na jihar Adamawa, Dakta Raymond Chidama, wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar na jihar, ya yaba wa shugabannin gangamin bisa zaɓen Adamawa a matsayin wurin fara wannan shiri.

Masu shirya gangamin sun ce taron wani ɓangare ne na dabarar neman goyon baya a faɗin ƙasar gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

Wai Trump ya nemi afuwar Tinubu kan wasu zarge zarge? Ga abin da aka binciko

Sun ce shirin zai mayar da hankali wajen jawo matasa, mata, ƙwararru da shugabannin al’umma, tare da jaddada muhimmancin ci gaba da manufofi, zaman lafiya da wadata.

Shugabannin Fulani sun goyi bayan Tinubu

An ji cewa shugabannin Fulani, Ardo Fulbe, ƙarƙashin jagorancin Ardo Aliyu, sun bayyana goyon bayansu ga ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.

Shugabannin sun bayyana matsayinsu ne yayin ziyarar girmamawa ga Darakta-Janar na Arewa for Asiwaju, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, a ofishinsa da ke Maitama, Abuja.

Taron ya mayar da hankali kan tattauna hanyoyin da shugabannin Fulani za su bayar da gudummawa wajen ganin Tinubu ya sake lashe zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.