Ana Shirin Zaben 2027, Shugaban INEC Ya Mika Dukan Lamuransa ga Ubangiji
- Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yi magana mai kama hankali yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027
- Amupitan ya jaddada cewa fasahar AI ba za ta tantance wanda zai lashe zaɓen 2027 ba, domin ’yan Najeriya ne ke da ikon zaɓe
- Ya bayyana cewa INEC ta kammala ayyuka 10 cikin 14 na jadawalin zaɓe, tana kuma ƙarfafa fasaharta domin gudanar da zaɓe mai inganci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya yi magana kan zaben 2027.
Amupitan ya ce ya miƙa komai ga Ubangiji yayin da yake fuskantar nauyin gudanar da babban zaɓen Najeriya na 2027.

Source: Facebook
Imanin da shugaban INEC ya yi ga Ubangiji
Amupitan ya bayyana hakan ne ranar Laraba a taron Artificial Intelligence and Democracy Forum 2026 da aka gudanar a Abuja, cewar Vanguard.
Farfesa Amupitan ya ce imaninsa da Ubangiji ne ginshiƙin ƙarfinsa yayin fuskantar nauyin ofishinsa.
Ya ce:
“Ana yawan tunatar da ni girman aikin da ke gabana. Haka kuma, kalmar Allah tana ƙarfafa ni, wadda take cewa, ‘Ku zo gare ni, dukanku masu wahala da masu fama da kaya masu nauyi, ni kuwa zan ba ku hutu.’ Wannan ita ce madogarar ƙarfina.
“Wani lokaci mutane suna cewa, ‘Ba ka damuwa da abin da ke faruwa.’ Sai in ce musu, na miƙa komai ga Allah.”
Shugaban INEC ya yi wannan jawabi ne a taron da ƙungiyar Yiaga Africa ta shirya, mai taken “Kare Zaɓen 2027 a Zamanin Fasahar Ɗan Adam ta Artificial Intelligence.”

Source: Twitter
INEC ta magantu kan fasahar AI a zabe
Da yake jawabi ga mahalarta taron, Amupitan ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa fasahar AI ba za ta tantance sakamakon babban zaɓen 2027 ba, yana mai jaddada cewa ikon zaɓen shugabannin ƙasar yana hannun masu zaɓe ne.

Kara karanta wannan
Tinubu na tsaka mai wuya, jigon APC ta aika wasika ga shugaban Amurka kan zaben 2027
A cewarsa, duk da cewa AI za ta iya yin tasiri ga bayanan da masu zaɓe ke samu, harkokin gudanar da zaɓe da sadarwar siyasa, dole ne fasahar ta kasance kayan aikin ƙarfafa dimokuraɗiyya, ba na raunana ta ba.
Ya ce:
“A’a, hakan ba zai tantance ƙuri’un zaɓen 2027 ba, kuma bai kamata su taɓa yin hakan ba. Zaɓin wanda zai jagoranci Najeriya yana hannun ’yan Najeriya ne kawai.
“Saboda haka, aikinmu a wannan taro da kuma cikin hukumar shi ne tabbatar da cewa AI ta kasance mai yi wa dimokuraɗiyya hidima, ba ita ce ke mulkinta ba.”
Amupitan ya bayyana cewa zaɓen 2027 zai ƙunshi masu rajistar zaɓe sama da miliyan 103, a rumfunan zaɓe 176,846 da ke jihohi 36 na tarayya da birnin Abuja,cewar Punch.
INEC ta fadi dalilin cire sunan Pantami
A wani labarin, an ji cewa hukumar INEC ta bai wa jam’iyyu wa’adin ranar 24 ga Oktoba domin sanar da ita korafe-korafen cire sunayen ‘yan takararsu.
Ta ce wa’adin ya yi daidai da Sashe na 32(2) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya bai wa jam’iyyun kwana 14 domin sanar da ita idan suna ganin an yi kuskure.
Daga cikin waɗanda ba a saka sunayensu a jerin ba akwai ‘yan takarar gwamnan Gombe da Ogun na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami da Oladipupo Adebutu.
Asali: Legit.ng
