Shugabannin Fulani Sun Fitar da Matsaya kan Wanda Za Su Yi Tsakanin Atiku, Tinubu
- Shugabannin Fulani, Ardo Fulbe, ƙarƙashin jagorancin Ardo Aliyu, sun bayyana goyon bayansu ga ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.
- Shugabannin sun bayyana matsayinsu ne yayin ziyarar girmamawa ga Darakta-Janar na Arewa for Asiwaju, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, a ofishinsa da ke Maitama, Abuja.
- Taron ya mayar da hankali kan tattauna hanyoyin da shugabannin Fulani za su bayar da gudummawa wajen ganin Tinubu ya sake lashe zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugabannin al’ummar Fulani, waɗanda aka fi sani da Ardo Fulbe sun bayyana wanda za su zaba a shekarar 2027.
Kungiyar ƙarƙashin jagorancin Ardo Aliyu, sun bayyana goyon bayansu ga ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani rahoto da wakilin Legit Hausa ya samu wanda shafin Biyora Online TV ya wallafa a Facebook a yau Alhamis 15 ga watan Oktobar 2027.
Tinubu ya kaddamar da kwamitin kamfen 2027
Wannan lamari na zuwa ne bayan Bola Tinubu ya kaddamar da kwamitin kamfen zaben 2027 a Abuja inda ya ba su shawarwari da jan hankalinsu.
Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da kwamitin kamfen APC na 2027, inda ya bukaci mambobinsa su hada kai.
Yayin bikin, Kashim Shettima ya soki Atiku Abubakar da Peter Obi kan kalamansu, yayin da Nentawe Yilwatda ya bayyana shirin kwamitin.
Hope Uzodimma da wasu manyan ‘yan siyasa sun nuna goyon bayan sake zaben Tinubu, tare da yabawa manufofin gwamnatin.
Menene matsayar shugabannin Fulanin a 2027?
Shugabannin sun bayyana matsayinsu ne yayin wata ziyarar girmamawa da suka kai wa Darakta-Janar na Arewa for Asiwaju (A4A), Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, CON, mni, a ofishinsa da ke Maitama, Abuja, ranar Laraba.
Taron ya mayar da hankali kan tattaunawa game da hanyoyin da shugabannin Fulani za su bayar da gudummawa ga ƙoƙarin ganin Shugaba Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.
Ko a zaben 2023 ma, kungiyoyin Fulani da dama ciki har da Miyetti Allah sun bayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu domin samun nasara.
Hakan ya biyo bayan kammala mulkin marigayi Muhammadu Buhari wanda yana daga cikin kabilar Fulani a Najeriya.
Marigayin ya bar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023 bayan nasarar Bola Tinubu inda aka rantsar da shi a Abuja.
Martanin Accord kan saka Adeleke a kamfen Tinubu
Mun ba ku labarin cewa wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar Accord sun bukaci Gwamna Ademola Adeleke ya fayyace masu matsayinsa kan kwamitin kamfen Bola Tinubu.
Wannan ya biyo bayan jin rahoton nada shi jagoran kamfen din Bola Tinubu a Osun duk da bai cikin APC da ke mulki a Najeriya.
Sun ce matakin na iya raunana jam’iyyar tare da rage damar ‘yan takararta da za a shiga zaben 2027 da su saboda suke neman ya fitar da matsayarsa kan lamarin.
Asali: Legit.ng

