Wai Trump Ya Nemi Afuwar Tinubu kan Wasu Zarge Zarge? Ga Abin da Muka Binciko
- Wasu rahotanni sun bulla a kafofin sadarwa cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, bai nemi afuwa ga Shugaba Bola Tinubu
- Bincike ya gano cewa hoton bidiyon da aka wallafa a shafukan sadarwa da ya nuna Trump yana magana kan matsalar tsaro
- An kuma gano cewa asusun X da ya wallafa labarin ba na uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu, ba ne, don haka ikirarin ƙarya ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A ranar Laraba, 7 ga Oktoba, 2026, an yi ta yada wani rahoto cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya ba Bola Tinubu hakuri.
Rahotanni suka ce wai Trump ya nemi afuwar Bola Tinubu ne bayan zarge-zargen da ya yi kan Najeriya game da ta'addanci.

Source: Twitter
Ƙarairayin da ake yi ta yaɗawa
Wani mai amfani da shafin X mai suna @OluremiTinubu ya yi ikirarin cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya nemi afuwar Bola Tinubu.
Wannan wallafa ta ƙunshi hoton wani labarin talabijin da aka ce ya nuna Trump yana neman afuwar.
Rubutun da aka sanya tare da hoton ya ce:
"Donald Trump ya nemi afuwa ga Shugaba Tinubu kan zarge-zargen da ba su da tushe da ya yi a shekarar da ta gabata, a cewar Trump, ‘ya yi kuskure game da alhakin hukumomin Najeriya kan matsalar ta’addancin da ake fuskanta a ƙasar’.”
Binciken da aka gudanar kan jita-jitar
Binciken Dubawa ya bayyana cewa wasu masu amfani da X sun amince da ikirarin a cikin tsokacinsu, yayin da wasu suka soki wallafar, wasu kuma suka bayyana cewa ƙarya ce.
Wani mai amfani da shafin mai suna @TheOjovi ya rubuta cewa:
“Shi ɗan amshin shatan su ne. Suna son su ba shi damar fita daga wannan matsala cikin sauƙi, domin ya ci gaba da lalata Najeriya. Dole Tinubu ya tafi.”
Wani mai sharhi mai suna @KENNYROSSY_097, wanda ya danganta asusun da uwargidan shugaban ƙasa, ya ce:
“Babban abin kunya ne idan OluremiTinubu ta fito tana yaɗa bayanan ƙarya ga jama’a! Jama’a ba wawaye ba ne kamar yadda kuka ɗauka a shekarun baya. Yanzu idanunsu a buɗe suke.”
Bayan yada rahoton a Facebook, an yi amfani da hanyar binciken asalin hoton, wato reverse image search, domin gano inda hoton da mai ikirarin ya wallafa ya fito.
Sakamakon binciken ya kai ta ga wani bidiyo da kafar World Source News ta wallafa a shafin X ranar 31 ga Agusta, 2026.
Bayanin da aka sanya tare da bidiyon ya nuna cewa Donald Trump yana magana ne kan mashigar ruwan Hormuz, ba kan matsalar ta’addanci a Najeriya ba.
Shin da gaske Trump ya nemi afuwar Tinubu?
Bayan tabbatar da cewa hoton da aka wallafa yana da alaƙa da wani lamari daban, an duba shafin Shugaba Trump na gaskiya, wato Truth Social.
Ta gano wata wallafa makamanciya da Trump ya yi ranar 30 ga Agusta, 2026, inda ya soki Iran.
Bincikenya nuna cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, bai nemi afuwa ga Shugaba Bola Tinubu kamar yadda aka yi ikirari ba.
Binciken ya kuma tabbatar da cewa an sauya hoton da aka wallafa tare da ikirarin domin ya dace da labarin da ake son yaɗawa.
Trump ya rubuta wasika ga Tinubu
An ji cewa Donald Trump na Amurka ya yaba wa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kan jajircewarsa wajen yaki da ’yan ta’adda.
Shugaban na Amurka ya ce dangantakar Amurka da Najeriya na da muhimmanci wajen yaki da ta’addanci.
Donald Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da Najeriya kan hadin gwiwar tsaro domin dakile ayyukan 'yan ta'adda.
Asali: Legit.ng


