APC Kano: 'Ayyukan da za Su Jawo wa Tinubu Ruwan Kuri'a a 2027'

APC Kano: 'Ayyukan da za Su Jawo wa Tinubu Ruwan Kuri'a a 2027'

  • Jam'iyya mai mulki ta APC ta bayyana yakinin cewa akwai wasu manyan ayyuka da Bola Ahmed Tinubu ya yi da zai jawo masa soyayyar jama'a a zaben 2027
  • Jam'iyyar reshen jihar Kano ce ta bayyana haka, tare da cewa manyan ayyukan gwamnatin tarayya za su taimaka wajen samun gagarumar nasara
  • Mai magana da yawun jama'a da APC a jihar Kano Auwalu Soja ya zayyano wasu daga cikin wadannan ayyuka da ya ke ganin sun yi wa jama'a dadi sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta bayyana cewa manyan ayyukan ci gaba da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa su na yi wa jama'a dadi.

Jam'iyyar ta ce tana da yakinin wadannan ayyuka za su taimaka masa samun gagarumar nasara a babban zaben shekarar 2027 duk da sukar da jam'iyyun adawa ke yi.

Kara karanta wannan

"Ba gaskiya ba ne": APC ta karyata cewa 'ya'yanta sun koma wajen Kwankwaso

APC reshen jihar Kano ta ce jama'a za su zabi Tinubu
Gwamnan Kano tare da shugaba Bola Tinubu yayin wata ziyara zuwa Abuja Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

Jaridar Tribune ta wallafa cewa Sakataren yada labaran APC na jihar Kano, Auwalu Soja, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano.

APC ta ce Tinubu yana aiki

Ya ce ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a sassan Arewacin Najeriya sun nuna kudurin gwamnatin Tinubu na bunkasa yankin, kuma sun karyata zargin cewa an yi watsi da Arewa.

A cewar Auwalu Soja, daga cikin manyan ayyukan gwamnatin tarayya akwai aikin bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK).

Ya kara da cewa haka kuma akwai layin dogo na zamani daga Kaduna zuwa Kano har zuwa Maradi, wadanda ke bi ta wasu yankunan karamar hukumar Kumbotso.

Kakakin jam'iyyar ya ce wadannan ayyuka shaida ne karara cewa gwamnatin Tinubu na zuba jari a yankin Arewa, don haka zarge-zargen masu suka cewa an ware yankin ba su da tushe.

Gwamnatinmu za ta kara himma - APC

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin Tinubu ta ce kan ba hukumar bogi kudi, bude asusu a CBN

Auwalu Soja ya kuma ce APC a Kano za ta kara himma wajen wayar da kan masu kada kuri'a domin tabbatar da shugaban kasa Bola Tinubu da gwamna Abba Kabir Yusuf sun samu miliyoyin kuri'u domin wa'adi na biyu a zaben 2027.

APC ta ce gwamnatin Tinubu ta yi ayyuka a Arewa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu yana jawabi a wani taro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Haka kuma, ya yaba wa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ayyukan da ya ce suna amfani kai tsaye ga al'umma, ciki har da gina tituna da shirye-shiryen tallafawa mata da matasa domin su dogara da kansu.

Sakataren yada labaran APC ya kuma musanta rahotannin da ke cewa wasu daga cikin 'yan jam'iyyar a karamar hukumar Kumbotso sun koma NDC.

Gwamnan Kano ya aika sako ga lauyoyi

A baya, mun kawo labarin cewa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya zaburar da lauyoyi game tabbatar da nasarar babban zaben 2027 da ke tunkaro Najeriya wajen tsaya wa a kan gaskiya.

Gwamnan, da ake yi wa lakabi da Abba Gida Gida ya bayyana cewa lauyoyi suna da matukar muhimmanci wajen tabbatar da dimokuradiyyada adalci a tsarin shari'a musamman wadanda suka shafi zabe.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kuma yi karin bayani game da matasan lauyoyi sama da 70 da ya dauka aiki tare da aiwatar da inganta iliminsu a jihar, inda ya ce ana sauke nauyi wajen biyan alawus-alawus a kan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng